A ’yan kwanakin nan, a matsayina na malamin jami’a ni kaina kuma a matsayina na uba, wanda ke da ’ya’ya mata har guda biyu, na ci karo da wasu labaru guda biyu da suka kara kidima ni kuma suka tayar mani da hankali; musamman dangane da yadda aka bar tantirancin wasu malaman jami’a na gudana ba tare da daukar matakin magance bahallatsar ba. Ina magana ne game da yadda wasu malaman jami’a a Najeriya ke wa dalibai mata cin zarafi da nuna fin karfi ta bangaren neman fasikanci da su.
daya daga cikin labaran, na ci karo da shi ne a ranar 10 ga watan nan, inda abokaina a dandalin Facebook da na Twitter suka rika bayyana yadda aka yi wa wani malamin jami’a kamun kazar kuku, a yayin da yake kokarin yin fasikanci da wata dalibarsa, bayan ya yi mata alkawarin kwarara mata maki a lokaci jarabawa. Malamin, mai suna Ifeayi Ugwu Raphael, yana koyarwa ne a Jami’ar Jihar Delta. Abin kunya, tsirara aka ritsa shi, haihuwar uwarsa. Yanzu dai hotunan tsiraicinsa suna ta ambaliya a intanet!
Kamar yadda labarin bahallatsar ya zo mani, shi malamin jami’ar, ya yi ta kokarin neman yin lalata da dalibar ne a can baya, amma ta ki ba shi hadin kai. Dalili ke nan ya kayar da ita jarabawa, a lokacin da take cikin shekararta ta biyu a jami’ar. A lokacin da ta shiga ajin karshe kuma tana bukatar ta ci kwas din malamin, sai ta tuntube shi, ta shaida masa cewa ya fadi duk abin da yake so, madamar zai tsallakar da ita siradin kwas din nasa. Shi kuwa, ganin cewa abin nema ya samu, wai matar direba ta haihi mota, bai bata lokaci ba ya shaida mata cewa jikinta yake bukata.
Ashe ba nan gizo ke saka ba, domin kuwa dalibar nan bai san kofar rago ta yi masa ba. Tun kafin ta amince da bukatarsa, ashe ta tsgunta wa abokan dalibtarta maza irin matsalar da ta samu. Dalili ke nan suka shirya mata dabarar da za su yi masa. Shi ne ta gayyace shi zuwa dakinta, ta ce a can za ta biya masa bukatarsa. Yalai kuwa, gogan naka sai ya bi ta zagaro-zagaro zuwa dakin, kamar rakumi da akala. Bayan ya shiga dakin, ya tube suturunsa kaf, ya koma haihuwar innarsa, sai dalibai maza da suka buya a dakin suka bayyana. Nan take suka dauki hotunansa a yadda yake, suka antaya su cikin kogin intanet, asiri ya tonu!
Kwana daya da faruwar wamnnan mummunan al’amari, sai kuma ga wani labarin shigen wancan. A wannan karon, labarin wani Farfesa ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, mai suna Festus Dabid Kolo, wanda kotu ta yanke wa daurin watanni biyu saboda kama shi da laifin bibiyar wata matar aure, wacce kuma ke dauke da juna biyu.
Shi ma dai kofar rago aka yi masa har asirinsa ya tonu. Kamar yadda labarin yake, ita ma wanban mace mai ciki, daliba ce a jami’ar. Kafin a kai ga kama shi, Farfesan ya yi ta bibiyar matar ne da kiran waya, alhali yana boye lambarsa. Daga bisani kuma ya rika aika mata da sakonnin tes masu dauke da kalaman batsa da motsa sha’awa. Kan haka dai har ya kai ga gayyatarta zuwa wani gidan shakatawa.
A rashin saninsa da wautarsa, bai san da cewa ’yan sanda da mijin matar sun yi kwantan bauna suna jiransa ba. Haka dai shi ma rashin sa’arsa ta cafke shi, domin kuwa shi ma yana yanayin tsiraici, haihuwar mahaifiyarsa aka rutsa da shi, yana nufin murkushe matar mutane, mai dauke da juna biyu! Wani abin takaici ma shi ne, mijin matar nan shi ma fa malami ne a Jami’ar ta Ahmadu Bello. Ke nan abokin aikinsa ne, amma ya zabi ya ci amanarsa.
Wadannan labarai biyu, babu abin da suke mana ishara sai irin yadda badala da iskanci suka zama ruwan dare a jami’o’inmu na Najeriya. Jami’o’inmu sun zama wata da’ira ta shedana da cin zarafin mata. A kasarmu, babu wani uban yarinya da ba ya dari-dari da tura diyarsa jami’a, musamman saboda yana da yakinin cewa tamkar ya tura tunkiyarsa ne zuwa turakun kuraye!
Idan abin ya yi kamari ma shi ne, yanzu malaman jami’ar, ba wai kawai ma fasikanci suke da daliban nasu mata ba, munin ya kai ga cewa wasu ma har kawalci suke yi, suna tallata daliban ga fasikan attajirai. Ni kaina na taba sanin wani malamin jami’a da ya saba kawalcin kyawawan dalibansa mata, yana hada su da manyan jami’an sojoji, su kuma suna saka masa da makudan kudi. Yadda yake ta’annatinsa shi ne, yakan gayyaci irin wadannan jami’ai ne su zagaya ajin da yake koyarwa, da zarar sun ga yarinyar da ta yi musu, sai su sanar da shi. Daga baya shi kuma zai kira ta, ya shaida mata cewa ta je wuri kaza ta hadu da wannan jami’in soja domin ya yi lalata da ita. Duk dalibar da ta yi tirjiya, babu abin da zai mata sai barazana, cewa zai kayar da ita, idan jarabawa ta zo. Kan haka dalibai suka tattara hujjoji, suka kai kararsa ga hukumar jami’ar. Bayan ya amsa laifinsa, kuma ba a yi masa komai ba, sai dai kashedi kawai aka ba shi.
Shin haka za a zauna ana kallon jami’o’inmu suna balbalcewa? Hakan bai dace ba, kamata ya yi Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta kasa da kungiyar Malaman Jami’a za su zauna su fito da dokar da za ta haramta wannan mummunar dabi’a domin ceto jami’o’inmu daga zama balbalcewa.
Annobar tantiran malaman jami’a a jami’o’inmu 1
A ’yan kwanakin nan, a matsayina na malamin jami’a ni kaina kuma a matsayina na uba, wanda ke da ’ya’ya mata har guda biyu, na…