Kimanin karin mutum 20 suka sake mutuwa sakamakon barkewar annobar amai da gudawa a Jihar Kebbi.
Cutar wadda ake kamuwa da ita sakamakon shan gurbataccen ruwa ta bazu zuwa kauyen Tungar Buzu da Korama da Samanaji da Keri a garin Shinaga da birnin Kebbi da Fakai da kuma garuruwan da ke cikin kananan hukumomin Koko da Besse a jihar.
A ranar Litinin din da ta gabata wata yarin mai suna Maryam Umar, ’yar kimanin shekaru 14 a duniya ta rasu sakamkon tsananin gudawa da amai a garin Tungar Buzu.
Haka nan a kusa da kauyen Kardi mutum uku sun mutu sakamakon gudawa ba kakkautawa.
Wani mazaunin garin Tungar Buzu, Abdullahi Usman ya shaida wa wakilinmu cewa mutanen kauyukan suna cikin fargaba saboda yadda annobar cutar ke bin garuruwansu daya bayan daya.