Daya daga cikin angwayen da Gwamnatin Kano ta yi wa auren gata ya zargi iyayen amaryarsa da hana ta tarewa da kuma neman ya sake ta.
A watan jiya ne Gwamnatin Kano ta yi wa mutum 1,800 auren gatan ciki har da ango Umar Ibrahim da amarya tasa da suka kwashe tsawon lokaci suna soyayya kafin a daura aurensu.
Umar ya bayyana cewa tunda aka daura aurensa da amaryarsa iyayenta suka hana ta tarewa inda suka dage cewa sai ya yi mata lefe kafin ta tare.
“Tunda aka daura aurenmu iyayen matata sun hana ta tarewa, wai dole sai na yi mata lefe.
“Ni kuma na ce ba zan yi ba saboda na san cewa babu batun lefe a wannan tsarin na auren gata,” in ji Umar.
- Samanja: Tauraron wasan kwaikwayo ya rasu yana da shekaru 84
- Duk wadanda muke bi bashi sai sun biya — MTN
Ya kara da cewa a halin da ake ciki iyayen matar tasa suna neman sai ya sake ta, amma shi ba zai saki amaryar tasa ba sai iyayenra sun biya shi kudaden da ya kashe a lokacin bikin.
“Ko da zan sake ta sai an biya ni wasu kudadena. Akwai Naira dubu 150 na kudin zancen da na bayar tunda farko.
“Akwai kuma kudina Naira dubu 17 na shinkafar da ta dafa a lokacin bikin, sannan akwai N65,000 na kwalliya da na ba ta,” in ji shi.
Sai dai duk kokarin Aminiya don jin ta bakin amarya Ummulkhair Salisu ya ci tura, domin duk kiran da aka yi wa wayarta ta ba ta tafiyar.
Shi ma mahaifinta, Malam Salisu ya yi gum da bakinsa, inda ya umarci wakiliyarmu da ta je Hukumar Hisbah don samun cikakken bayanin abin da ya faru.
Darakta-Janar na Hukumar Hisbah, Dokta Abba Saidu Sufi ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma hukumar na kokarin ganin bangarorin sun daidaita.
Sai dai ya ce babu kanshin gaskiya a cikin zargin da angon ke yi wa surukansa.
“Gaskiya ne har yanzu amaryar ba ta tare ba, sai dai babu gaskiya a cikin maganar da angon yake zargin surukansa. A yanzu haka muna kokari wajen ganin an shawo kan lamarin cikin sauki ”
Idan za a iya tunawa a ranar 13 ga watan Oktoba Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa maza da mata 1800 auren gata wanda ta ce ta yi ne don magance ayyukan alfasha a tsakanin al’umma da kuma taimaka wa iyayen da ba su da karfin aurar da ’ya’yansu.
Kafin daurin auren gwamnatin ta ware Naira Miliyan 850 da ta saya wa amaren kayan daki da kayan abinci da kuma jarin da aka bayar ga amaren domin dogaro da kansu.