Mutum ɗaya ya riga mu gidan gaskiya yayin da wani ango ya zargi amaryarsa da zuba guba a abincin baƙi a wani liyafar ɗaurin aure a ƙaramar hukumar Jahun da ke Jigawa.
An kwantar da ango a asibiti da ke tsananin rashin lafiya bayan cin abincin bikin da ake zargin amaryarsa da zuba guba a ciki.
Wannan ɗaurin aure da ya rikiɗe zuwa abin tausayi bayan ana zargin amarya cewa ta kawo musu abinci mai guba a wurin liyafar aurenta.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana wa jaridar PUNCH Online cewa, mai yiwuwa ne wani ne ya sa amaryar ta aikata hakan.
Da yake magana da PUNCH Online a ranar Juma’a, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce ana gudanar da bincike.
“Mun samu rahoton cewa amaryar ta kawo abinci mai guba da aka ci a liyafar ɗaurin auren, wanda hakan ya sa angon ya fara rashin lafiya.
“‘Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin zuba guba a cikin abincin a yayin bikin auren a jihar,” in ji Adam.
Ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin su biyun amarya ne da wata mace guda, inda ya ƙara da cewa suna tsare kuma ana yi musu tambayoyi daga sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa, “Zamu yi duk abin da za mu iya don ganin an yi adalci.”
A cewar kakakin rundunar ’yan sandan, an sallami dukkan waɗanda suka halarci ɗaurin auren da suka ci abincin mai gubar daga asibiti, sai dai mutum guda da aka tabbatar ya mutu.
“Yanzu haka rundunar tana gudanar da bincike kan lamarin, kuma zamu yi ƙarin bayani nan gaba.