Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekara 45, ya gamu da ajalinsa a hannun ɗan uwan matarsa, mai suna Magaji Salisu saboda karbar bashin gishiri na Naira 20.
Ɗan marigayin, Ibrahim Zakari, ya ce rigima ce ta kaure tsakanin mahaifinsa da kanin matarsa, lamarin da ya kai ga mutuwar mahaifinsa.
- Saurayi ya kashe kawunsa da bindigar kakansa a Bayelsa
- Na gargaɗi Ningi kan zargin cushen N3.7trn a Kasafin Kuɗin bana — Ndume
Ibrahim ya ce, an samu saɓanin ne a lokacin da mahaifinsa ya dawo daga kasuwa, sai matarsa Sadiya Salisu ta shaida masa cewa ta karɓi bashin gishiri na naira 20, lamarin da ya fusata mahaifinsa da a baya ya yi gargaɗi game da karɓar kowane irin bashi daga wurin kowa.
Ibrahim ya ce rigimar da ta faru tsakanin marigayin da matarsa ta kai ga yin musayar kalamai.
Ɗan ya ce mahaifinsa ya koma shagonsa ya kira ƙanin matarsa a waya ya shaida masa duk abin da ya faru a gida tsakaninsa da matarsa.
An yi zargin cewa ɗan uwan matar ya fusata ya zo gidan yana neman mijin ‘yar uwarsa, amma bai same shi a gida ba.
Daga nan ne ya yanke shawarar ya bi shi zuwa shagonsa da ke ‘Yan shinkafa a Karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano.
Ɗan marigayin ya ƙara da cewa, nan take Magaji yana yin arba da mahaifinsa, sai ya fara dukansa har ya kai ga ƙashin ƙirjinsa ya karye.
Ya ce sun kai mahaifinsu wani asibiti da ke kusa da garin Kura inda likita ya yi masa magani ya sallame shi, amma bayan komawarsu gida sai mahaifinsa ya rasu.
Ibrahim ya ce sun kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda kuma jami’in ‘yan sanda na Kura ya gayyaci matar da ɗan uwanta kuma yanzu haka ana bincike a kan lamarin.
Ya roƙi kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano da ya tabbatar wa mahaifinsa adalci.
Ya zuwa lokacin tattara rahoton babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan jihar ta yi a kan lamarin.