A gurfanar da wani magidanci a gaban Kotun Majistare da ke Rijiyar Zaki da ke Kano bisa zarginsa da laifin bata sunan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar. ’Yan sanda ne suka kai wanda ake zargin mai suna Labaran Mai Aski wanda aka fi sani da Hayaki Fid-da Na-Kogo, mazaunin Unguwar Mandawari gaban kotun, inda suka shaida wa kotun cewa a ranar 15 ga watan jiya, wanda ake zargin ya shiga gidan rediyon Rahama ya bata Matiamkain Gwamna, Farfesa Hafizu Abubakar, inda ya ce wai Mataimakin Gwamnan ya yi zagon kasa ga jam’iyya ya bayar da umarnin a zabi wata jam’iyya ba APC ba a zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar a watan Fabrairu.
Takardar karar ta ce “A cikin kalamanka kai Labaran ka ba Mataimakin Gwamnan tsoro tare da barazanar cewa za ku kore shi daga APC.”
To amma wanda ake zargin ya musanta laifuffukan tsoratarwa da barazana da bata suna da yada labaran karya. Lauyansa, Barista Usman Fari ya roki kotun ta bayar da belinsa, rokon da Lauyan Gwamnati, Barista Nura Sa’id ya yi suka a kansa.
Alkalin Kotun Mai shari’a Aminu Usman Fagge ya bayar da belin Hayaki Fid-da-Na Kogo bisa sharadin sai mai Unguwar Mandawari ya zo gabanta sannan ya zama ya biya harajin shekara uku tare da tantance takardun harajin. Idan kuma wanda ake tuhumar ya gudu to masu tsaya masa su za su biya Naira dubu 500 Kotun ta sanya ranar 11 ga Afrilu 2018, don ci gaba da sauraren karar.