An kama wasu mata ’yan aiki su biyu bisa zargin satar sarka da kudinta ya kai Naira miliyan 20 mallakar uwar dakinsu.
A ranar Alhamis aka gurfanar da matan gaban Kotun Majistaren Ebute Meta a Jihar Legas bisa zargin hadin baki da sata.
Sai dai ’yan aikin sun musanta zargin da ake musu na sace sarkar.
Jami’i mai tuhuma, Cyril Ejiofor, ya fada wa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Yuni, a unguwar Ikoyi.
Ya ce matan sun hada baki suka sace sarkar uwar dakinsu wadda darajarta ta kai miliyan N20, sannan suka sayar.
A cewarsa, hakan ya saba wa sassa na 287 da 411 na Kundin Dokokin Jihar Legas.
Alkalin kotun, A. Kayode-Alamu, ta ba da belin matan kan N500,000 kowaccensu tare da shaidu bibbiyu.
Daga nan, ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ran 24 ga watan Agusta.