✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin wani da dukan Shugaban Karamar Hukumar Fagge

Kotun Majistare ta 36 da ke Nomansland a Kano ta ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi a tsakanin wani matashi mai suna Shamsu…

Kotun Majistare ta 36 da ke Nomansland a Kano ta ci gaba da sauraren shari’ar da ake yi a tsakanin wani matashi mai suna Shamsu Habibu Kwaciri da ake zargi da dukan Shugaban Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Tun farko an zargi matashin ne da hada baki da wadansu katti inda suka yi wa Shugaban Karamar Hukumar Fagge, Alhaji Ibrahim Abdullahi Shehi dukan kawo wuka.

Shamsu Habibu ya musanta laifuffukan da ake zarginsa da su wadanda suka hada da hadin baki da cin zarafi, laifuffukan da suka saba wa sashe na 97 da na 234 cikin kundin shari’a na Pinal Kod.

Alkalin kotun, Mai shari’a Umma Sani Kurawa ta ba da belin wanda ake kan Naira dubu 100 tare da kawo mutum biyu da za su tsaya masa, sannan ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Nuwamban bana.