✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin ta da kashe jaririyar kishiyarta

Yan sanda a Kano sun kama wata matar aure mai suna Binta Hassan a unguwar Darmanawa ta karamar Hukumar Tarauni bisa zargin kashe jaririyar kishiyarta…

Binta Hassan wacce ake zargi da kashe jaririyar kishiyartaYan sanda a Kano sun kama wata matar aure mai suna Binta Hassan a unguwar Darmanawa ta karamar Hukumar Tarauni bisa zargin kashe jaririyar kishiyarta mai kwana daya da haihuwa.
Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis din makon jiya, lokacin da Binta wadda ita ce amarya ta je barkar haihuwar jaririyar da kishiyarta mai suna Sadiyya ta haifa a gidansu da ke unguwar Darmanawa.
Rahotannin sun ce tun asali akwai takun-saka a tsakanin kishiyoyin biyu inda aka ce mako biyu kafin azumi sun yi rigima da juna lamarin da ya jawo maigidansu ya kore su, daga baya ya dawo da Binta ita kuma uwargida Sadiyya wacce ke da tsohon ciki ta zauna a gidan iyayenta har zuwa lokaci da ta haihu wannan waki’a ta auku.  
Sai dai Binta mai kimanin shekara 21 da take tsare a ofishin ’yan sanda na Hausawa ta musanta zargin da ake yi mata inda ta bayyana wa Aminiya cewa duk abin da ake fadi a gari karya da sharri aka yi mata don a bata mata suna. “A ranar Alhamis wato kwana daya da haihuwar jaririyar da kishiyata Sadiyya ta haifa sai na shirya bayan Sallar Magariba na tafi yi mata barka da yake unguwa daya muke da gidan iyayenta. Da zan tafi na yi sallama da maigidana wanda ke fama da zazzabi a lokacin na tafi yin barka tare da biyu daga cikin ’ya’ya hudu na kishiyar tawa. Bayan mun je gidan mun yi wa mai jego da iyayenta barka har mun yi sallama za mu tafi gida sai saurayin kanwarta da ake kira Hajiya ya zo inda ya nemi a kai masa jaririyar ya gani. Har ina yi mata wasa cewa duk abin da aka samo na jaririyarmu ne. Da na fito kofar gida sai na ga jaririyar a hannun Hajiya a zaune sai na ce ta ba mu jaririyarmu kada sanyi ya kama ta, na karbe jaririyar da niyyar mayar da ita cikin gida, amma ina kokarin sa kafata a cikin gidan sai na yi tuntube da tudun kofar shiga gidan kafata ta gurde, har kakar jaririyar ta hango ni tana tambaya ta abin da ya faru. Da na mike kasancewar kafata tana zafi sai na ba babban dan kishiyar tawa mai suna Walid jaririyar na ce masa ya kai ta cikin gidan. Daga nan ya fito muka tafi gida. A lokacin da na ba da jaririyar lafiyarta lau, sai dan kuka da ta yi na jin zafin faduwar da muka yi, “ inji ta.
Malama Sadiyya mahaifiyar jaririyarMalama Binta ta kara da cewa “Ban fi minti 20 da dawowa gida ba sai na ji ana buga kofar gidan kamar za a balla ta, na yi zaton ma almajirai ne don haka na zo na bude kofar a fusace. Ina budewa sai na ga iyalan gidan kishiyata suna cewa wai na je barka na kashe musu jaririya. Maigidana ya jiyo hayaniya ya fito da ya ji abin da suke fadi sai ya hau fada ya ce da su su tafi su bar masa gida wannan magana karya ce. Daga nan sai aka gaya min cewa wai sun ce za su je gidan iyayena su kai kara ta na kashe musu ’ya. Jin haka ya sa na tafi gidan namu a unguwar Karkasara sai dai da na je ban same su ba, ashe gidan iyayen mijinmu suka fara zuwa. Ina nan a gidanmu sai ’yan sanda suka zo suka kama ni zuwa nan.”        
Wadda ake zargin da ke goye da danta mai wata goma da haihuwa ta ce ta dauki wannan al’amari a matsayin kaddara.
Sadiyyya mahaifiyar jaririyar ta bayyana wa Aminiya cewa duk da akwai takun-saka tsakaninta da amaryarta ba ta taba zaton za ta aikata haka ba, shi ya sa ma da ta zo mata barkar ta karbe ta hannu bibbyu. “Bayan ta zo barka mun karbe ta hannu bibbyu sai muka zauna a daki muna hira. A nan ne ma take sanar da ni cewa wai wani yaro Sabo dan makwabtanmu zai zo min barka. Ni kuwa ganin cewa yaron ba ya yi min magana sai na ce mata me zai zo ya yi, sai ta ce wai barka zai zo yi min. Har ta yi shiri za ta tafi sai saurayin kanwata Hajiya ya zo zance inda ta dauki jaririyar ta kai masa. A nan ne muka rika cewa idan an samo abin barka namu ne. Daga nan sai muka yi sallama da Binta, har ta kai soro sai ta dawo wai kudinta zun zube, don haka sai aka ba ta fitila don ta haska, da ta je sai ta dawo ta ce ba ta gani ba. Sannan ta tafi. Ni ban san abin da ke faruwa ba sai dai kawai kawo min yarinya aka yi a galabaice. Da na karbe ta sai na ga yawu a gefen bakinta, ga hawaye a gefen idonta, tana wani irin numfashi. Sai na kira babata na nuna mata. Muka fara dudduba jikinta inda na ga wasu huji uku a kasan kirjinta da jini. Muna rike da ita sai ta ja numfashi sau uku shi ke nan ba ta sake yin motsi ba. Ina kyautata zaton a wannan lokaci rai ya yi halinsa,” inji ta.
Ita ma kanwar mai jegon mai suna Amina wacce aka fi sani da Hajiya ta bayyana yadda abin ya faru cewa ta ga lokacin da kishiyar yayarta ta sanya yariyar a hijabinta ta tsuguna a kofar gida, sai dai ba ta yi zaton wani mugun abu take aikatawa a wannan lokaci ba. “Da yake ina kofar gida a lokacin da ta fito za ta tafi gida sai ta tsaya a gefen gidanmu da na tambaye ta dalilin tsayuwarta sai ta ce wai wani makwabcinsu Sabo take jira zai zo barka.

Daga nan sai ta karbi jaririyar daga hannuna wai za ta mayar da ita cikin gida saboda sanyi. Da ta zo daidai kofar gidanmu sai na ga ta tsuguna da jaririyar a cikin hijabinta sai na tambaye ta abin da ke faruwa, amma sai ta yi min shiru, sau uku ina tambayarta sannan ta ce min wai gurdewa ta yi ta fadi. Daga nan sai ta dago sai ta ba Walid ya mayar da ita gida. Sannan ya fito suka tafi gida. Ni dai ina kofar gida sai aka zo aka kira ni cewa wai jaririyar ta mutu,”
inji Hajiya.            
Amina (Hajiya) kanwar mahaifiyar jaririyarDuk kokarin Aminiya don jin ta bakin mijin matan Malam Salisu Abdullahi wanda direban mota ne a kamafanin man fetur na A.A. Rano ya ci tura.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce zuwa yanzu sun fara bincike a kan lamarin kuma za su mika lamarin ga ofishin CID na jihar da zarar sun samu sakamakon binciken likita daga asibiti. Ya ce batun da wacce ake zargi ta yi cewa ta fadi da jaririyar a hannunta, har an samun raunuka biyar a jikin jaririyar yayin da ita kuma ba ta ji ciwo ko daya ba abin tambaya ne.