Wasu da ake kyautata zaton matsafa ne sun sace wani yaro dan shekara 12 da haihuwa, mai suna Yunusa Umar (Alhaji), bayan sun kashe shi kuma suka cire idanunsa da harshensa da wasu abubuwa a cikinsa da faratansa da jijiyoyin hannunsa da kafarsa, a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna.
Da yake yi wa wakilinmu bayani yadda wannan abu ya faru, mahaifin yaron, Malam Umar Aliyu Liman (Baba Babba) ya bayyana cewa shi dai wannan yaro, a ranar da ya bata, ya tafi makarantar haddar Alkara’ani ce da yake zuwa da safe da kuma bayan Azahar.
Ya ce a wannan rana ya tafi da safe ya dawo misalin karfe 12, na rana. Da ya dawo mahaifiyarsa ta ce ya cire rigarsa a wanke, ta ba shi tallar cincin ya kai wa masu gini a nan kusa da gidansu. Sai dai tun da wannan yaro ya fita, ba a sake ganinsa ba.
Mahaifin ya ce sun yi neman yaron sun gaji amma ba su gan shi ba, shi ne suka dauki hotansa suka sanya a shafukan yanar gizo suna cigiya. “Ba mu ji labarinsa ba sai da aka yi kwana 6 muna nemansa, sai wani yaro ya kira ni a waya ya ce in zo gida. Bayan da na dawo gida a guje sai na sami labarin cewa akwai wani maharbi mai sanya ashuta a bayan gari, don kama makwarai, ya je don duba ashutar da ya sanya, sai ya ga mutum kwance a wajen. Nan take da na je sai na ga wannan yaro ne a mace. An kwakule masa idanuwansa, an cire masa harshe, an fasa kansa, an debi wani abu, an fasa cikinsa an debi abin da za a iya diba, an yanke al’urarsa, an cire faratansa baki daya, an cire jijiyoyin hanunsa da agararsa, an ajiye masa robar cincin dinsa da takalmansa da kudin cinikin da ya yi Naira 70 a waje guda.”
Malamin ya yi kira ga hukuma da ta tsaya ta yi aikinta na kare rayukan jama’a domin hakkin jama’a yana kanta. Ya ce a halin da ake ciki, irin wadannan abubuwa suna ta faruwa a ko’ina a Najeriya amma ba a daukar wani mataki sai dai a bar talakawa su dauki doka a hanunsu.
Da aka tuntubi Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu, ya bayyana cewa sun sami labarin faruwar wannan al’amari kuma suna nan suna bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki, don gurfanar da su a gaban kotu.