✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin malami da rubar da hannun almajirinsa

Ana zargin wani alaramma mai suna Malam Nafi’u Gomo mazaunin garin Gomo a Karamar Hukumar Sumaila ta Jihar Kano da rubar da hannayen almajirinsa mai…

Ana zargin wani alaramma mai suna Malam Nafi’u Gomo mazaunin garin Gomo a Karamar Hukumar Sumaila ta Jihar Kano da rubar da hannayen almajirinsa mai suna Hassan Sa’idu mai kimanin shekara 9, wanda  ya fito daga garin Birnin Kudu a Jihar Jigawa saboda ya gaza kawo masa harajin Naira 40.

Aminiya ta samu labarin cewa Malam Nafi’u yana aika almajiransa bara inda kowane almajiri yake kai masa Naira 40 kullum.

Majiyarmu ta ce da almajiri Hassan bai kai masa Naira 40 din ba ne sai Malam Nafi’u ya daure masa hannu da roba tsawon kwana biyu lamarin da ya yi sanadiyyar rubewar hannyensa  biyu.

Hassan Sa’idu ya shaida wa Aminiya cewa malaminsa ya yi amfani da danko ne ya daure masa hannuwansa biyu. “Mun je bara ban kawo wa Malam Naira 40 ba saboda ban samu ba, sai ya ce karya nake yi, don haka ya daure min hannayena da danko har tsawon kwana biyu sannan ya kwance ni,” inji shi

Kungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya reshen Jihar Kano (FIDA) a karkashin shugabancin Barista Huwaila Muhammad Ibrahim ta nemi Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya kamo malami don gurfanar da shi a gaban kotu.

Kuma a wata takarda da aka raba wa manema labarai Kwamishinan Shari’a na Jihar Jigawa Barista Musa Adamu Aliyu ya nemi Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtar ya dauki matakin gurfanar da Alaramman a gaban kotu.