✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin malaman makaranta da kashe dalibinsu da duka a Zariya

Aminiya ta gano an masa hukuncin ne saboda fashin zuwa makaranta

Ana zargin Shugaban malaman makarantar Al-Azhar Academy da ke Kofar Bayan a Zariyan Jihar Kaduna, da mataimakinsa da kisan wani dalibinsu ta hanyar lakada masa duka.

A ranar Juma’a 20 ga watan Oktoban 2023 ce dalibin mai suna Marwanu Nuhu Sambo, dan ajin JS3 ya rasa ransa ta hanyar hukuncin da hukumar makarantar ta dauka a kansa.

Aminiya ta ziyarci gidan iyayen dalibin da ya rasu, wato gidan Alhaji Sambo da ke unguwar Kofar Kuyanbana cikin birnin Zariya.

Isa Sa’idu, daya ne daga cikin iyalan da ya bayyana mana yadda lamarin ya faru inda ya ce, “A jiya da safe abokin mahaifin marigayi ya dauke shi zuwa makarantar sakamakon marigayin ya daina zuwa, wai saboda an koma da shi ajin baya don haka ya ce baya son makarantar.

“Wanda ake zargi da aikata kisan ya ce ya damka marigayin a hannun Mataimakin Shugaban makaratan, kuma ya ce tun a gabanshi ya fara dukan marigayin.”

‘An yi masa bulala sama da 100’

Malam Isa, ya kara da cewa a bayanin da suka samu daga abokan karatun dalibin a makarantar shi ne an gabatar da shi a gaban daliban aka yi masa bulala kusan 100, daga nan kuma aka kai shi ofishin Shugaban Makaratan, inda a nan ma aka sake tube masa riga aka ci gaba da dukan shi har sai da wasu daga cikin hakoransa suka fice daga bakinsa.

Daga nan da suka ji ba ya numfashi sai suka kai shi hanyar suka shimfidar da shi, sannan suka kai shi asibiti.

Bayanan da Aminiya ta samu na nuni da cewa duk da mutuwar wannan dalibi, mahukuntar makarantar ba su sanar da iyayensa ba har sai da iyayen yaron suka rika jin rade-radin cewa an kai shi asibitin Al-Ridha Clinic da ke kusa da makarantar.

“A nan ne suka garzaya asibitin domin su tabbatar da gaskiyar labarin. Da isar su asibitin sai likitan da ya duba yaron ya tabbatar musu da cewa shi ne ya duba yaron, kuma gawa aka kawo musu, ba mara lafiya ba,” in ji Isa.

Da wakilinmu ya ziyarci makarantar domin tabbatar da gaskiyar lamarin, ya tarar da makarantar a kulle saboda yau [Asabar].

Sai dai mun zanta da wasu daga cikin daliban makarantar da suka kai ziyarar ta’aziyya gidan abokin karatun marigayin.

Daya daga cikin yaran wanda suke aji daya da dalibin kuma muka sakaya sunansa, ya ce, “Mataimakin Shugaban Makarantar shi ya zo da yaron gaban “assembly” inda suka rika yi masa bulala babu kakkautawa tare da Shugaban Makarantar, tun muna iya kirga bulalar har muka bata lissafi, ko ni na kirga bulala akalla 105 wanda aka yi wa marigayin a gabanmu,” in ji dalibin.

“Daga nan kuma suka wuce da shi zuwa ofishin Shugaban makarantar, suka cire masa riga, suka bar shi da gajeren wando kawai suka ci gaba da dukansa har yaron ya yi yunkurin guduwa, amma aka sa shuwagabannin daliban makarantar suka rike shi suka koma da shi, aka ci gaba da dukansa har sai da suka cire masa hakora, suka kashe shi,” in ji shi.

‘A kan rashin zuwa makaranta aka yi masa hukuncin’

Aminiya ta gano cewa ana zargin an yi wa dalibin hukuncin ne saboda dalibin ba ya son zuwa makaranta kullum saboda kunya da yake ji na komawa da shi ajin baya da aka yi smasa akamakon rashin yin kokari a aji.

“Bayan sun kashe Marwanu sai suka fito da gawar waje, suka ajiye shi a hanyar zuwa bandaki har aka tashi makaranta,” in ji dalibin.

Sai dai har zuwa lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan mahukuntan makarantar ba su ziyarci iyalan mamacin ba domin jajanta musu.

Za mu bincika gaskiyar lamarin – Gwamnati

Shugaban Hukumar Tantance Ingancin Makarantun Jihar Kaduna, Dokta Abubakar Usman, wanda ya ziyarci gidan da tawagarsa ya ce sun je ne domin tantance gaskiyar lamarin da ya faru.

Ya kuma sha alwashin cewar za su tabbatar da hakan bai sake faruwa ba a nan gaba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da kama mutum biyu da ake zargi da aikata kisan, kuma suna ci gaba da bincike a kai.