Hukumar Kula da Walwala da Jin Dadin Jama’a na karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna ta kama wani magidanci mai suna Usman Umar da ake zarginsa da azabtatar da ’yarsa mai shekara uku tare da karairaya ta.
Yarinyar mai suna Maimuna Usman da mahaifanta suna zaune a Unguwar Kusfa cikin birnin Zariya.
Babbar Daraktar Hukumar, Hajiya Ramatu Tanko ta shaida yi Aminiya cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 11:00 na rana, dangin mahaifiyar Maimuna suka kai kara cewa mahaifin ’yar yana neman hallaka ta, “Kuma sun zo tare da ’yar kamar yadda ka gani tana da karaya a wuri biyu a cinyarta ta dama da kuma kafadarta ta hagu, kuma duk jikinta akwai shaidar bulala da raunika. Daga nan muka sanar da ’yan sanda aka je aka zo da mahaifin, ita kuma yarinya muka kai ta asibiti,” inji ta.
Kakar yarinya kuma mai rikonta mai Suna Balaraba ta shaida wa wakilinmu cewa: “Ni ce na haifi mahaifiyar yarinya, kuma ni ce nake rikonta, domin tun tana ciki da wata hudu auren mahaifan ya kare ta dawo gida. A dakina aka haife ta har lokacin da mahaifiyarta ta sake yin wani auren tana hannuna, kuma har Allah Ya yi wa mahaifiyarta rasuwa wajen haihuwa wata 10 da suka wuce tana hannuna.”
Ta ce da Sallah kakanta wanda ya haifi mahaifinta ya ce a kai ta, ta yi musu Sallah a gidansu, domin sunan matarsa aka sa mata. “To bayan an kai ta sai mahaifinta Usman ya dauke ta daga gidan Babansa ya kai ta gidansa, kuma bayan gama bikin Sallah zuwana biyu domin in dauko ta amma sai ya hana in gan ta, har ma ta kai ga yana gaya mana cewa ya kai ta Bauchi can wajen dangin mahaifiyarsa, ashe ba haka ba ne tana daki ya kulle ta ba ya bari a gan ta. Da muka samu labari ne sai muka tura maza zuwa wurin kakanta mahaifin Usman, domin shi ya ce a kai ta. Mahaifin ya ba dan umarni cewa ya dawo mana da ita amma ya ki. To muka je gidan muka samu matarsa mai suna A’isha da ’ya’yanta uku suna cin abinci muka tambaye ta yarinyar, sai ta ce ai an kai ta can wurin kakarta a Bauchi. Muna cikin haka sai ya shigo ya ce ba ta nan, mu kuma muka ki tafiya tunda mu samu labarin yana kulle ta a daki. Da ya shiga wani daki sai muka bi shi ashe yarinyar tana ciki a kulle an kakkara mata duwatsu, kuma an rataya mata layu a wuya. Sai muka ce ya ba mu ita, sai ya ki, shi ne muka kai kara ofishin kula da walwalar jama’a suka sa ’yan sanda suka kama shi, mu kuma aka kawo mu nan asibitin aka kwantar da mu aka yi hoto tare da ba mu magunguna,” inji ta.
Da wakilinmu ya tambayi Maimuna wa ya yi mata wadannan raunuka sai ta ce: “Baba da Inna!” wato mahaifinta da matarsa da ya aura daga baya.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci ofishin ’yan sanda na kofar Fada a Zariya ranar Litinin Baban Jami’in ofishin, Abdul Kasim ya tabbatar da faruwa lamarin kuma ya ce ya kammala bincike ya tura su kotu.
A kotun, wakilinmu ya ruwaito cewa wakilin Kwamishinan ’Yan sanda, Abdullahi Sarki ne ya gabatar da wanda ake tuhumar inda aka zarge shi da yin amfani da karfi wajen duka da cin mutuncin yarinya, wanda hakan laifi ne a karkashin sassa na 263 da 265 da 266 da kuma 241 na dokokin aikata manyan laifuffuka (CPC).
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin da ake yi masa, inda Alkalin Kotun Mai shari’a Umaru Bature ya tura shi gidan yari zuwa ranar Litinin mai zuwa, inda za a ci gaba da sauraren shari’a.
Shugabar kungiyar Tallafa wa Yara da Mata da Yaki da Cin Zarafinsu, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim, ta nuna gamsuwa da yadda kotun ta fara daukar matakin hukuta mahaifin yarinyar. Ta ce tura shi gidan yari da kotun ta yi na mako guda, ya nuna yadda kotu ta dauki matakin kwato wa yarinyar hakkin cin zarafinta da ya yi.
Ta bayyana niyyar kungiyarsu ta tallafa wa yarinyar ta hanyar samar mata da gudunmawar kudin magani a asibiti, inda ta ce, tuni kungiyar ta kashe fiye da Naira dubu 100 don nema mata lafiya.
Wata ma’aikaciyar gidan rediyon DITb, mai suna Halima Aliyu kofar Doka, ta sha duka a hannun matar wanda ake zargin wato A’isha Usman lokacin da take kokarin jin na bakinta kan zargin da ake yi cewa ita da mijinta ne suka yi wa Maimuna rubdugu. Sai matar ta fusata a kan sa sunanta a bugun yarinyar, inda ta sa aka yi ma ma’aikaciyar duka tare da yayyaga mata hijabinta.