Jami’an’ yan sanda a Jihar Oyo sun kama mutum uku ciki har da wani korarren limami bisa zarginsu da mallakar sassan jikin mutum inda suke zargin sun kashe shi tare da daddatsa shi domin yin tsafi a garin Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Wani faifai bidiyo da Aminiya ta yi arba da shi ya nuna limamin da sauran mutum biyu sanye da ankwa a hannu a harabar Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (CID) da ke Iyaganku a Ibadan inda suke tattara sassan jikin mutumin da ake zargin sun kashe.
- Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MDD
- Abin Da Ke Jawo Zargin Allurar Riga-Kafi Da Cutarwa
Wata majiya ta ce mutanen da aka kama, sun yaudari mutumin da suka kashe ne cewa za su samar masa aikin yi suka dauke shi a cikin motarsu zuwa wani daji a garin Moniya a Karamar Hukumar Akinyele inda suka hallaka shi.
Majiyar ta ce asirinsu ya tonu ne a hanyarsu ta komawa kauyen Apete inda suka yi kicibis da shingen bincike na jami’an tsaro wadanda suka tsananta bincike bayan sun hango jini na zuba daga cikin motarsu.
Bayan ’yan sanda sun kama su ne bincike ya gano cewa daya daga cikinsu yana rike da mukamin Mataimakin Limamin Babban Masallacin Awotan a kusa da kauyen Apete a Karamar Hukumar Ido.
Sai dai wata majiya daga masallacin ta ce tuntuni Majalisar Malaman Masallacin ta kori mutumin mai suna Malam Taofeek Kabelohun tare da nada Malam Abdulhakeem Abdulrasheed ya maye gurbinsa.
Majiyar ta ce “Biyu daga cikin wadanda aka kama wato Taofeek Kabelohun da Rahman Muibi a baya an taba kama su kan zargin aikata irin wannan danyen aiki na tsafin neman duniya da sassan jikin mutum.”