An gurfanar da wani Fasto mai suna Fasto Samuel John a gaban Kotun Majistare ta 10 da ke Nomansland a Kano bisa zargin sa da yi wa tagwaye da wata yarinya fyade.
Mai gabatar da kara Sufeto Shu’aibu Musa ya shaida wa kotun cewa wani mutum mai suna Sylbester Osehi da ke zaune a Layin Festing Road ne ya kai kara ofishin ’yan sanda cewa Fasto John ya yaudari ’ya’yansa uku wadanda yake turawa gidan Faston a Layin Wather-head a Unguwar Sabon Gari da niyyar Faston ya yi musu addu’a inda ya yi amani da wannan dama ya yi musu fyade.
Takardar karar ta ce “A wani lokaci da yaran suka je gidanka suka tarar matarka ba ta nan, sai kai Samuel John ka dauki tagwayen (an sakaya sunansu) masu shekara 13 ka kai su kan gadon matarka ka yi lalata da su. Sannan ka juya kan kanwarsu (an sakaye sunansu) ka rika shasshafa sassan jikinta.”
Fasto Samuel John ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su na fyade da cin zarafi ,wadanda suka saba da sashe na 283 da 268 na kundin Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Maryam Ahmad Sabo ta bayar da umarnin a tsare Faston a gidan maza zuwa ranar 26 ga watan Satumban bana don ci gaba da sauraren shari’ar.
A wani labarin kuma Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Alhaji Rabi’u Yusuf ya nuna damuwa kan yadda ake samun yawaitar laifuffukan fyade a jihar, inda ya nanata cewa rundunarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ana yin hukunci mai tsanani ga wadanda aka samu da aikata wannan laifi.
Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da rundunar ta gabatar da wadansu mutane da ake zargi da laifin fyade da luwadi ga kananan yara maza da mata da aka kama a lokuta daban-daban.
Ya ce rundunar ta samu kararraki kan laifukan fyade har guda 34 kuma an kama wadanda ake zargi mutum 35. Ya ce akwai yara maza da mata 36 da suka gamu da wannan cin zarafi na fyade inda ya ce akwai koke-koken zargin aikata fyade 15 da za su duba domin daukar matakin da ya kamata a kai.
Alhaji Rabi’u Yusuf ya bukaci jama’a su kara lura da yadda ’ya’yansu suke mu’amala da mutane koda akwai dangantaka a tsakaninsu, domin a cewarsa wasu laifuffukan fyaden da ake samu za a ga akwai nasaba a tsakanin wanda ake zargin da yaran. “Yana da kyau iyaye da masu rikon ’ya’ya su snya ido sosai a kan aboka huldar ’ya’yansu maza da mata,” inji shi.