A ranar Asabar din da ta gabata, wani dalibi dan aji uku (shekarar karshe) mai suna Muhammad Ali Sango a Babbar Makarantar Sakandiren Fasaha ta Ungogo a Jihar Kano ya rasa ransa sakamakon dukan kawo wuka da ake zargin ’yan uwansa dalibai suka yi masa.
Saddiku Ali Sango da ke unguwar dorayi, Kano dan uwan marigayin ne, wanda ya yi wa Aminiya karin haske game da yadda suka samu labarin rasuwar kanin nasu. Ya bayyana cewa shugaban makarantar ne ya kira babansu, ya gaya masa cewa marigayin ba shi da lafiya, yana kwance a Asibitin Waziri Gidado. “Da shugaban makarantar ya gaya wa mahaifinmu wannan magana ta waya sai muka dunguma muka tafi asibitin. A can ne yake sanar mana cewa wai yaronmu ya rasu sakamakon duka da masu kwacen waya suka yi masa a ranar Juma’a, a lokacin da ya fita sayen katin waya. Da muka nemi gawa sai suka ce tana ofishin ’yan sanda na Ungogo.
“Da muka isa, DPO ya dauko littafin tattara bayanai, ya karanta mana abin da ya faru cewa an kai gawar asibiti, ganin irin raunukan da ke jikin gawar, likitan ya ce ba zai bayar da gawar ba sai da ’yan sanda. Nan dai aka kira ’yan sanda na Ungogo suka dauki gawar zuwa ofishinsu,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Da aka fito mana da gawar yaron, babu kyan gani domin irin raunikan da aka yi masa; ga shaidar bulala rudu-rudu nan kwance a jikinsa, ga shi an yanka masa jiki da abu mai kaifi, ga shi kuma an karya masa cinya.”
dan uwan marigayin ya musanta batun da shugaban makarantar ya yi, cewa masu kwacen waya ne suka yi sanadiyyar mutuwar yaron a ranar Juma’a. A cewarsa, a ranar Asabar marigayin ya kira mahaifinsa a waya. “Muna da ja kan cewa a ranar Juma’a aka yi wa marigayin wannan ta’asa, domin a ranar Asabar da safe misalin karfe shida da rabi marigayin ya kira mahaifinmu, inda mahaifin namu yake ba shi hakuri, cewa ba zai samu damar kai masa ziyara ba sakamakon zai je wajen kaninsa a wata makarantar daban. Kuma har suka gama hira, mahaifinmu bai ji alamu na rashin lafiya a tare da yaron ba. Hakan ya sa ya yi mamaki da aka kira shi da daddare ranar Asabar din cewa yaron yana kwance a asibiti babu lafiya.”
Har ila yau, iyaye da ’yan uwan marigayin sun nemi hukuma ta bi masu hakkin dansu na ransa a wurin wadanda suka kashe. “Muna nemna hakkin ran yaronmu, domn idan har mutane za su rika sarayar da hakkin ran dan uwansu da aka kashe a irin wannan hanya, to babu shakak ba su taimaki al’umma ba, domin sun goyi bayan a ci gaba da aikata irin wanann barnar a kan wasu mutane
da ba su ji ba ba su kuma gani ba. Don haka muna neman hakkin ransa, ba za mu yafe ba. Muna so ya zama izna ga na baya don su guji aikata irin wannan al’amari a nan gaba.”
Malam Ahmad Tijjani Abdullahi shi ne Shugaban Hukumar Makarantun Sakandaren Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano. Ya bayyana cewa tuni hukumarsu ta kafa kwamiti don bincikar gaba dayan al’amarin. “Kamar yadda kika ji labarin nan haka abin ya kasance, wato bayanai biyu ke fita game da kisan. An ce fita marigayin ya yi wajen makaranta don sayen kati, duk da mun san cewa rike waya a makaranta ba daidai ba ne. Sannan an ce su ma ’yan uwansa dalibai sun yi masa duka,” a cewar shugaban.
DSP Magaji Musa Majiya, Kakakin ’Yan sanda a Jihar Kano ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa tuni suka fadada bincike a kan lamarin inda zuwa yanzu ta kama dalibai biyar da ake zargi da kisan yaron, kasancewar an same su da laifin dukansa a wannan rana da ya rasu.