Ana zargin cutar coronavirus ce ta kashe wani likita mai suna Dakta Dominic Essien, kuma malami a tsangayar Tsarin jiki da ke jami’ar Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.
Dakta Dominic, ne mamallakin asibitin San Dominique da ke rukunin gidaje na Ewet a cikin garin Uyo, ya mutu ne a asibitin kwararru na Ibom Multi-Specialist kuma asibitin yana daya daga cikin cibiyar killace masu dauke da cutar Coronavirus a jihar.
Rahotanni na bayyana cewa, marigayin yana dauke da zazzabin da cutar mura da kuma kalubalan shakar nunfashi na tsawan mako guda, hakan yasa ake saka masa na’urar shakar nunfashi a asibitinsa.
Daga bisani ne aka maida shi asibitin kwararru na Ibom Multi-Specialist, don likitocin da ke kula da masu dauke da cutar COVID-19 su lura da shi, an yi masa gwajin cutar da ke damunsa.
- Coronavirus: Gwamnatin Katsina za ta rufe masallatan Juma’a
- Dokar hana fita: Kwalliya na biyan kudin sabulu?
Dakta Dominic, ya mutu kafin a kammala gwaje-gwajen don tabbatar da matsayinsa ko yana dauke da COVID-19.
A cewar shugaban kungiyar likitoci (NMA) reshen jihar Dakta Nsikak Nyoyoko, ya bayyanawa manema labarai ranar Juma’a cewa, har zuwa lokacin da likitan ya rasu ba a kammala tantance abin da ya kashe shi ba.