✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin Boka da yi wa matar aure ciki a Bauchi

ya yi mata cikin ne lokacin da ta je nema wa 'yarta magani

’Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani boka da ake zargi da yi wa wata matar aure ciki a lokacin da ta kai ’yarta neman magani a wajensa.

Kakakin rundunar a jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce wanda ake zargin mai kimanin shekara 32 na karamar hukumar Tafawa Balewa, ya yi amfani da kayan maye ne wajen gusar da hankalinta kafin ya yi mata fyaden.

Wakil ya kuma ce sun kama wani malamin makaranta mai kimanin shekara 25 da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekara bakwai fyade a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Ya ce, “Bayanan da ’yan sanda suka tattara sun nuna cewa wanda ake zargin, mazaunin unguwar Ajiya a garin na Alkaleri, malami ne a wata makaranta mai zaman kanta a garin.

“Jamia’nmu sun kuma kama wani mai sayar da askirin a garin Bauchi, saboda zargin yin luwadi ga wani yaro mai shekara 12 a bayan wani banki a Alkaleri.

“Binciken farko-farko ya nuna wanda ake zargin ya sayi ruwan leda ne daga hannun yaron, sannan ya yaudare shi zuwa cikin wani shago ya yi lalatar da shi a ciki,” inji Kakakin ’yan sandan. (NAN)