Daruruwan al’ummar kasar Siriya sun gudanar da zanga-zanga don yin Allah wadai da yadda kasashen Larabawa ke kulla wata sabuwar dangantaka da gwamnatin Bashar al-Assad.
Boren da ya gudana a birnin Idlib na zuwa ne mako guda bayan da Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Saudiyya ya gana shugaba Bashar al-Assad birnin Damascus.
- Basarake ya rasu a hannun ’yan bindiga
- Air Peace zai kwaso daliban Najeriya da suka makale a Sudan kyauta
Bayanai sun ce wannan ziyara ta zama irinta ta farko a shekaru 12 bayan da yaki ya barke a kasar.
Kazalika jami’an diflomasiyyar kasashen Saudiyya da Tunisiya da Masar sun yi wata ganawa da ke da zummar lalubo hanyoyin kawo karshen yakin da ya daidaita kasar.
Siriyawan dai na neman kasashen duniya musamman na yankin Gabas ta Tsakiya da su ci gaba da mayar da shugabansu saniyar ware, saboda ba sa son kowacce kasa ta saka musu baki don ba za su taba daidaitawa da al- Assad ba.