✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zanga-zanga a Kaduna saboda karin kudin wutar lantarki

Yadda mutanen suka fito dauke da kwalaye rubuce da sakkoni ga kamfanin KEDCO.

A ranar Asabar mazauna rukunin gidajen Ministoci da ke Millenium City a jihar Kaduna, sun gudanar da wata zanga-zangar lumana don kawo musu dauki game da kudin wutar lantarki da kamfanin KEDCO ke karba daga wajensu.

Sun bukaci Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) da gwamnatin tarayya da su shiga tsakaninsu da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna domin su samu rangwamin kudin wutar da suke biya.

Shugaban kwamitin wutar lantarki na MPH, Abdulrauf Taha ya shaida wa Aminiya cewa “duk wata ana kawo mana takardar biyan kudi, kamar gida mai daki daya 170,000, mai daki biyu 250,000, mafi karancin da ake kawo mana shi ne 40,000.

“Don haka bamu gano da wane irin tsari ake amfani da shi ba wajen karbar kudin wutar lantarkin da muka sha ba,” a cewar Taha.

Masu Zanga-zanga

Mazauna yankin sun fito dauke da rubutu a manyan kwalaye inda suke bayyana bacin ransu da sakonni daban-daban.

Kazalika, a bayan nan ne mazauna yankunan Badiko, Unguwan Rimi da Apakwa suka yi korafi game da kudin wutar lantarki mai yawa da  Kamfanin rarraba wutar na Kaduna ke karba.

Wata mai suna Halima Rufa’i, ta bayyana cewa a baya tana biyan 10,000 duk wata yanzu kuma ya koma 38,000 duk wata kuma babu abin da ya sauya duk da korafin da ta shigar.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi jami’in sadarwa na Kamfanin KEDCO, Abdulazeez Abdullahi, ya ce dole ne a samu karin kudin wuta tunda samun wutar ya karu, kuma hakan ya faru ne saboda sabon tsarin da ake amfani da shi a yanzu.