✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zaman dar-dar bayan an yi wa manomi yankan rago a Zangon Kataf

Hankula sun tashi a Karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna bayan an gano wata gawa da aka yi wa yankan rago yashe a bakin…

Hankula sun tashi a Karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna bayan an gano wata gawa da aka yi wa yankan rago yashe a bakin rafi.

Ganau sun shaid wa Aminiya cewa tun jiya da yamma a garin Zango ake neman wani mutum da ya tafi gona da ba a ji duriyarsa ba sai wayewar garin yau Alhamis aka tsinci gawarsa yashe a bakin rafi an yi masa yankan rago.

“Da yammacin ranar jiya muna tafiya sai muka ga Jama’a sun yi cincirindo a bakin wani coci mu kuma ba mu san me ke faruwa ba, har gabanmu ya fadi amma muka wuce salin alin.

“Sai da safen nan kawai aka ce an ga gawar wani kabila da aka yi masa yankan rago a gona inda aka jefar da shi a bakin kogi.

“Daga nan kawai sai muka ga an fara sa shingaye ana tsare hanya ana kokarin tare motoci”, inji majiyar da ta bukaci a sakaye sunanta.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton majiyar ta shaida wa Aminiya cewa an ya yi cirko-cirko kafin daga baya sojoji da ‘yan sanda suka iso don kwantar da rikicin da ake tsoron ka iya tashi a garin da tun makon jiya ake zaman dar-dar kan rikicin filayen gonaki.

Yayin da jaridar Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya ce ba zai ce komai a kai ba tukuna amma a saurare shi zuwa wani lokaci