✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zaman dar-dar a mazabar Gawuna a Kano

Ana zaman firgici tun bayan da jami’an Hukumar DSS suka bar yankin.

A halin yanzu babu kwanciyar hankali yayin da ake shirin soma zabe a Unguwar Gawuna da ke Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.

A nan ne dai ake sa ran dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC kuma Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna zai kada kuri’arsa.

Sai dai gabanin tabbatuwar hakan, har jami’an ’yan sanda da aka baza a yankin domin shirin ko ta kwana sun bukaci karin ma’aikata, la’akari da yadda rikici zai iya fantsama a kowane lokaci.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan daba da suka yi lamo a yankin sun shiga taitayinsu yayin da jami’an Hukumar DSS suka hallara a wurin.

Amma dai bayan barin jami’an na DSS, yanayi na firgici ya sake mamaye yankin.

Jihar Kano dai na daya daga cikin Jihohin da tun kafin yanzu an yi hasashen za a yi gumurzu saboda tsananin adawa ta siyasa da ke tsakanin jam’iyyar NNPP da kuma mai mulki ta APC.

%d bloggers like this: