A ranar Alhamis ne ’yan Kuwait suke kada kuri’ar zaben ’yan majalisar dokokin kasar a karo na biyu, cikin kasa da shekaru biyu.
A watan Disambar shekarar 2020 ne dai Kuwait ta gudanar da zaben majalisar dokokin da aka rushe a watan Yunin shekarar, aka sake yin wani ba da jimawa ba.
- Ambaliya ta ci mutum 3, wasu 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi
- Kwastam ta kwace shinkafa da kayan N79m a Katsina
Mutane 313 ne dai da suka hada da mata, suka tsaya takarar ’yan majalisar a zaben wakilai 50, kuma za su shafe wa’adin wakilci na shekaru idan sun samu nasara.
Kafatanin masu fafatawar dai na takara ne a matsayin daidaikun mutane, kasancewar an haramta kafa jam’iyyun siyasa a kasar da ke da amintaka da Amurka.
Akalla ’yan kasar 796,000 ne za su kada kuri’a a rumfunan zaben da za a bude tsawon sa’o’i 12, kuma ana sa ran sakamakon zai fita a hukumance ranar Juma’a.
Kuwait dai ita ce kasa ta farko a kewayen yankin da ta taba kafa zababbiyar majalisar dokoki a shekarar 1963.
Sai dai duk da kasar na gudanar da zabukan ’yan majalisar dokokin, ikonta na hannun masarautar kasar, da kuma sarkinta da ke da alhakin nada mukaman gwamnati.