✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zaben neman kara wa shugaban kasa Karfin iko a Tunisiya

Al'ummar Tunisiya na kada kuri'a raba-gardamar kara wa shugaban kasar karfin ikon da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

Al’ummar Tunisiya na kada kuri’a raba-gardamar kara wa shugaban kasar karfin ikon da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

’Yan adawa na ganin zaben wata manufa ce ta shugaba Caid Saied na murkushe tsarin dimokuradiyya da ya kawo shi kan mulki bayan guguwar sauyin kasashen Larabawa da ya kawo shi kan mulki a 2011.

Ana gudanar da zaben ne a daidai lokacin da ake cika shekara guda bayan Shugaba Saied ya rushe majalisar dokokin kasar, ya kum ayyana dokar ta-baci.

Bangarorin ’yan adawar kasar sun bayyana matakin a matsayin juyin mulki da ke barazanar mayar da kasar zuwa zamanin mulkin kama karya da ta yi ban kwana da shi a 2011.

An samu karancin fitowar masu jefa kuri’a a safiyar Litinin a rumfar zabe ta Rue Marseilles da ke birnin Tunis.

Amma duk da haka, Illyes Moujahed, wanda shi ne mutum na farko a kan layin zabe ya ce kasar ba ta wata fata da ta fi Shugaba Saied.

“Na fito nan ne domin ceto kasar Tunisiya daga rushewa da kuma shekarun da ta yi tana fama da rashawa da kuma gazawa,” inji shi.

Kawo yanzu dai babu tabbacin lokacin da za a sanar da sakamakon zaben wanda ake sa ran kammalawa da karfe 9 na dare.

Akwai kuma karancin sha’awar jefa kuri’a a zaben a tsakanin ’yan kasar, kuma mayan jam’iyyun kasar sun kaurace msihi.

A sakamakon haka, masana na ganin shugaban kasar zai samu abin da yake so, sakamakon karancin fitowar masu zabe.

Wani dan kasar a birnin Tuni, Samir Slimane ya ce ba zai yi zaben ba, domin, “Ban tunanin za a samu sauyi; babu abin da Kais Saied sai sauya. So kawai ya zama shi ke da wuka da nama.”

Zaben raba-gardamar bai ta kayyade mafi karancin kason da ake bukata na masu jefa kuri’ar amincewa ba da sabon kudin tsarin mulkin sakar mai mutum miliyan 9.2 masu katin zabe.

Shugaban kasar dai ya ayyana cewa sabon kundin tsarin mulkin zai fara aiki ne da zarar an samar da sakamamkon.

Sai dai kuma bai bayyana abin da zai biyo baya ba idan jama’ar kasar sun yi fatali da sabon kudin zargin mulkin.

Saied ya bayyana sauye-sauyen nasa a matsayin ginshikin kasa sabuwar Jamhuriyar Tunisiya da za ta dora kasar a kan turbar da ta dace wajen kawo karcin matsalolinta na siyasa da tattalin arziki.