✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana yunkurin yanke hukuncin kisa kan masu fyade a jihar Neja

Yayin da matsalar fyade ke dada kamari a ‘yan kwanakin nan a Najeriya, Majalisar Dokoki ta jihar Neja na duba yiwuwar yin dokar yanke hukuncin…

Yayin da matsalar fyade ke dada kamari a ‘yan kwanakin nan a Najeriya, Majalisar Dokoki ta jihar Neja na duba yiwuwar yin dokar yanke hukuncin kisa da kuma daurin rai-da-rai ga masu fyade da dangoginsu ciki har da cin zarafin mata.

Majalisar ta kuma umarci Babban Mai Shari’a na jihar da ya ware kotuna na musamman domin hukunta masu aikata laifukan.

Yunkurin ya biyo bayan ‘Yar Majalisar Mai Wakiltar mazabar Gurara, Hon. Binta Mamman ta jawo hankalin takwarorinta kan bukatar daukar matakin gaggawa don dakile matsalar da yanzu ta tasamma zama ruwan dare a jihar da ma kasa baki daya.

Ta kuma yi Allah-wadai da irin yadda a ‘yan kwanakin nan rahotanni ke nuna yadda lamarin na kara kazancewa.

Ko a kwanan nan an ruwaito yadda aka ci zarafin wata tsohuwa mai kimanin shekaru 85 baya ga wasu ‘yan mata biyu da mahifinsu ya rika lalata da su kusan tsawon shekaru bakwai.

“Muna bukatar tsauraran matakai don hukunta irin wadannan mutanen. Yawancinsu sun aikata laifin ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Babban abin mamakin shi ne yadda ba wai mata kadai ake cin zarafi ba, a’a har ma da maza”, in ji ta.

“Amma idan muka tanadi hukunci mai tsaurin gaske kamar wannan, to za su fahimci cewa abin da suke aikatawa ba daidai ba ne”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa yayin gabatar da kudurin, Kakakin Majalisar, Hon. Abdullahi Bawa Wuse ya ce batun fyade da ayyukan cin zarafi annoba ce da ta fi ta coronavirus illa.

Ya kuma ce akwai bukatar a sake waiwayar dokar bincike saboda masu binciken wadannan laifukan na da jan aiki a gabansu wajen gurfanar da masu laifin.