Bayan kashe wasu al’ummar Arewa mazauna garin Orlu dake jihar Imo mutum Bakwai, hudu a garin Orlu, uku kuma a garin Amaka, har yanzu ’yan Arewa na fuskantar matsin lambar barin jihar.
Rahotanni sun ce mutanen na fuskantar matsin lambar ne daga hannun masu Fafutukar Neman Kafa Kasar Biyafara wato IPOB.
- ’Yan matan Chibok: Ina aka kwana bayan shekara 7?
- JAMB ta haramta wa iyaye raka ’ya’yansu wuraren zana jarabawa
Lamarin dai ya jefasu cikin firgici har inda ake kyautata zaton sama da mutum 60 sun tattatara ya nasu ya nasu suna barin jihar.
’Yan kungiyar ta IPOB dai suna bin kauyuka da lunguna a Owerri da kewayenta suna yiwa masu sana’ar sayar da nama kisan dauki dai-dai.
Dokta Lawan Yusuf, mazaunin garin Owerri ya shaidawa Aminiya cewa “Ko a jiya Juma’a ma sai da ’yan Biyafara suka kai wa wasu ’yan Arewa masu sayar da nama hari suka kashe mutum uku, kuma tuni muka yi jana’izarsu,” inji shi.
A duk inda suka tarar da dan Arewa wurin kasuwancinsa sukan tambayeshi “ko yana da bizar izinin shigowa kasar Biyafara? Idan mutum yace babu sai su kama shi sa suka har suna saransa, da haka wanda ajalinsa ke kusa har ya mutu”.
Ta fuskar samar da tsaro kuwa, Dokta Yusuf yace “In banda unguwar Hausawa wato Oma-Hausa, babu inda aka kai jami’an tsaro saboda tsagerun su kansu sun san basu isa su tunkari unguwar ba, baskiya dai ana cikin zaman zullumi”.
Ya zuwa yanzu dai, kimanin mutum 11 ke nan aka kashe ’yan Arewa a jihar ta Imo a cikin kasa da mako biyu.