An samu nasarar bankado wasu da ake zargi da samar da takardun shaidar boge na Kwalejin Kimiya Da Fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya.
Kantoman riko na makarantar, Farfesa Shehu dalhatu ne ya bayyana haka a yayin tattaunawarsa da Aminiya a Zariya. Ya ce sakamakun kama wani mutun daya da aka yi da ake zarginsa da samar da satifiket na jabu, wanda kuma ba ma’aikaci ba ne a makarantan, ya sa ya zuwa yanzu ’yan sanda sun kama mutane 25, wadanda ma’aikata ne a makaranta da ake zargin da sa hannunsu, inda yanzu haka ake bincike a kai.
Shugaban ya tabbatar wa Aminiya cewa ya samu tes na wayar hannu, ana yi masa barazanar za a halaka shi matukar bai dakatar da wannan binciken da ake yi ba. Ya ce har kudi suka hada, Naira dubu arba’in aka tara domin a tura tawaga zuwa Jami’ar Bayaro Kano don a binciko yadda yake tafiyar da aikinsa, da nufin fallasa wa duniya irin laifuffukan da ya aikata a jami’ar, kafin a ba shi Kantoman Kwalejin.
Ya ce duk wanda bincike ya tabbatar da sa hannunsa kan wannan badakala, makaranta za ta kafa nata kwamiti don ladabtarwa daidai da laifin da mutun ya aikata, kamar yadda doka ta tanada.
Wakilinmu ya tuntubi babban jami’in ’yan sanda na yankin domin karin bayani, ya ce shi ba zai ce komai ba. Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin ’yan sanda a Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu ta hanyar buga masa waya har sau biyu tare da tura masa sakon tes amma babu amsa.