✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana tuhumar ‘likita’ da yi wa mutane allurar cutar kanjamau

Jami’ai a India na gudanar da bincike kan ikirarin da aka yi cewa wani likitan bogi ya yi wa akalla mutum 33 allura da sirinji…

Jami’ai a India na gudanar da bincike kan ikirarin da aka yi cewa wani likitan bogi ya yi wa akalla mutum 33 allura da sirinji mai dauke da cutar HIb.

Ana zargin likitan bogin da yin amfani da sirinji da ya yi wa masu dauke da HIb allura wurin yi wa mutanen da ke fama da mura da tari a jihar Uttar Pradesh kamar yadda BBC ta ruwaito.

Jami’an kiwon lafiya na tarayyar kasar za su kai ziyara lardin Unnao, inda lamarin ya faru, domin gudanar da bincike kan batun.

An yi zargin cewa mutumin ya karbi kudin kasar, wato rupee goma kan kowacce allura da ya yi.

Har yanzu dai ba a tabbatar da adadin mutanen da ya yi wa allra da sirinjin ba. 

Wani likita da ke cikin masu binciken Dokta Tanymay Kakkad ya shaida wa jaridar The Indian Edpress cewa “Binciken likitoci ya nuna cewa yiwuwar kamuwa da cutar HIb tana kai 0.3% idan aka yi wa mutum allura da sirinjin da ke dauke da cutar saboda kwayar cutar ba ta jurewa yaduwa cikin iska.” 

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato jami’ai na cewa mutum 33 da aka tabbatar sun kamu da HIb na cikin mutum 566 da aka yi wa gwajin cutar a wani gangami da gwamnati ta hada.