✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana shirin tura Abba Kyari Amurka kan Badakalar Hushpuppi

Shugaban ’Yan Sanda ya ba Kyari takardar 'kweri' bayan rahoton kwamitin bincike.

Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar tura Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Abba Kyari zuwa kasar Amurka ya amsa tambayoyi kan zargin sa da hannu a Badakalar Hushpuppi bisa bukatar gwamantin Amurka.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ba wa Abba Kyari takardar tuhuma kan alakarsa da Ramon Abbas, wato Hushpuppi, wanda Amurka ke zargi da damfara ta intanet.

Wani babban hafsan dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, “Shugaban ’Yan Sanda ya ba wa Abba Kyari takardar tuhuma da neman bahasi bayan rahoton kwamitin bincike ya gano akalarsa da Hushpuppi, gami da wasu abubuwa da ya yi da suka saba tsarin aikin dan sanda”.

Wata kotu a Amurka dai ta bayyana Abba Kyari a cikin masu hannu a damfarar da Hushpuppi ya yi wa wani attajiri dan kasar Qatar.

Bayan zargin da hukumar bincike ta FBI ta kasar Amurka ta yi wa Abba Kyari, Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Najeriya ta dakatar da shi daga bakin aiki, Shugaban ’Yan Sanda kuma ya kafa kwamiti na musamman domin bincikar lamarin.

Babban hafsan dan sandan da muka zanta da shi ya ce duk da cewa kwamitin binciken da DIG Joseph Egbunike ya jagoranta ya gano Abba Kyari na da Hushpuppi, kwamitin bai ba da shawarar a tura Kyari zuwa Amurka ba, saboda kwamitin bai same shi da aikata wani laifi a Amurka ba.

“Babu wata shaidar da ke nuna ya aikata wani laifi a Amurka da zai sa a tura shi can. Hukumomin da suka dace ne ke da alhakin hukunta shi; Ofishin Babban Lauyan Gwamantin Tarayya zai ba da shawara game da ko ya dace a tura shi Amurka, amma da wuya,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya, Frank Mba, ya shaida mana ta waya cewa Shugaban ’Yan Sandan ya tura wa Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda rahoton da kwamitin ya gabatar masa a watan Agusta domin hukumar ta dauki matakin da ya dace.

“Kwamitin ya gabatar masa rahoton shi kuma ya tura wa hukumomin da suka dace, musamman Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda wadda a halin yanzu tan nazarin rahoton,” inji shi.

Da muka tuntubi Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ta hannun kakainsa, Umar Jibrilu Gwandu, ya ce mai gidansa zai yi magana a kan lamarin a lokacin da ya dace.

“Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya zai yi abin da ya dace daidai da abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada,” inji Gwandu.

Wani babban hafsan dan sanda ya ce abin da doka ta tanada shi ne Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Najeriya ce kadai za ta hukunta Kyari.

A cewarsa, hukuncin zai iya zama dakatarwa daga aiki, rage masa matsayi ko kuma kora daga aiki.

Amma wani masani kan harkokin tsaro, Kabir Adamu, ya ce ana iya gurfanar da ’yan sanda a kotu a kan zargin su da aikata manyan laifuka.