✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana neman dalibai 30, an ceto 180 bayan harin kwaleji a Kaduna

Ana jinyar daliban da suka samu rauni a wata cibiyar soji.

Kimanin dalibai 30 ne ba a gani ba yayin da take ci gaba da tattara alkaluma bayan harin ’yan bindiga da suka sace dalibai a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya (FCFM( da ke Afaka, a Jihar Kaduna. 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce harin kwalejin da ke daura da Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta NDA ya ankarar da sojoji da suka kai dauki tare da ceto mutum 180 bayan da arangama da ’yan taaddar. 

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ce: Sojin Kasan Najeriya sun ceto mutum 180, galibinsu daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, Karamar Hukumar Igabi, ta Jihar Kaduna.

Ya ce: “’Yan bindigar sun far wa kwalejin ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Alhamis suka yi awon gaba da dalibai da ma’aikata.”

Shugaban FCFM, Afaka, Dokta Usman Mohammed Bello ya tabbatar wa Aminiya cewa an kwashe daliban zuwa barikin sojoji ta Rundunar Sojin Kasa ta 1.

Sun kutsa kai cikin makarantar ta hanyar keta katangarsa sannan suka kutsa kai kimanin mita 600 don kai hari kan ginin farko,” inji Kwamishinan Tsaron. 

Ya ce bayan samun kiran neman agaji, Ma’aikatarsa ta sanar da Runduna ta 1 ta Sojin Kasan da kuma Rundunar Horas da Sojin Sama ta Najeriya.

“Dakarun sun yi nasarar kubutar da mutum 180; Dalibai mata 42, dalibai maza 130 da maaikata takwas.

“Akwai kuma karin dalibai 30, maza da mata da har yanzu ba a san inda suke ba.

Aruwan ya ce wasu daga cikin daliban da aka ceto sun ji rauni kuma ana jinyar su a wani sansanin sojoji.

Ya bayyana yabon Gwamna Nasir El-Rufai ga sojojin bisa hanzarin da suka yi da kuma kubutar da mutanen su 180.