✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana neman bakaniken da ya sare kan ’yarsa

’Yan sanda sun bazama wajen neman wani bakanike mai suna Albert Olaposi mai shekara 25 da ake zargi da sare kan ’yarsa mai suna Mercy…

’Yan sanda sun bazama wajen neman wani bakanike mai suna Albert Olaposi mai shekara 25 da ake zargi da sare kan ’yarsa mai suna Mercy a yankin Gbongan na Jihar Osun. 

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola ta tabbatar da lamarin da cewa rundunar na neman wanda ake zargin ruwa a jallo.

Kafin wanda ake zargin ya kashe ’yar tasa tana zaune ne a hannun kakarta a yankin Oke Oje a garin Gbongan yayin da iyayenta ke zaune a wani yankin na daban a garin.

Sai dai a ranar Litinin ta makon da ya gabata wanda ake zargin ya je gidan mahaifiyarsa inda ya dauki yarinyar ya kai ta wajen da ya sare mata kai.

Kakar yarinyar wato mahaifiyar wanda ake zargin ne ta ankarar da ’yan sanda halin da ake ciki, sai dai kafin su isa wajen ya tsere.

Ta ce an kai gawar yarinyar dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife a jihar.