✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kashe N211m wajen kwashe shara duk wata a Kaduna —Kwamishina

Kwamishinan ya roki mutanen jihar wajen yin tsafta.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce tana kashe naira miliyan 211 duk wata wajen kwasar shara a cikin manyan yankuna uku da ke  Jihar.

Kwamishinan Muhalli da Albarkatu, Mista Husseini Ibrahim ne ya bayyana haka ranar Asabar yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai NAN a Kaduna.

A cewarsa, Jihar Kaduna ce birni na uku mafi girma a Najeriya, wanda yake da adadin mutane masu yawa saboda akwai tarin shara da ake zubarwa.

Ya ce wannan shara mai tarin yawa da ke lakume makudan kudade, ana kwashe ta ne daga Zariya, Kafanchan da kuma birnin Kaduna.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta ba wa hukumomin kwashe sharar jihar damar samar da hanyoyin kwasar shara mafi inganci a fadin jihar.

Kazalika, ya roki jama’ar jihar da su taimaki gwamnatin jihar wajen samar da tsaftaccen muhalli.

Ya ce za a samu hakan ne kadai idan ana zubar da shara ta hanyar da ya dace, tare da kauce wa zubar da ita barkatai a wuraren da ba su dace ba

Sannan ya roki jama’a da suke ankarar da gwamnati kan wuraren da ake zubar da sharar ba bisa ka’ida ba.