Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa kimanin mutum miliyan 29 ne ke bukatar agaji a kasashen yankin Sahel, tana mai nuna yadda matsalar tsaro da yunwa ke kara ta’azzara a tsakanin al’ummomin kasashe shida na yankin da suka hada da Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Majalisar ta ce mutum miliyan 29 ke cikin tsananin bukatar gaggawa, ciki har da yara miliyan 1.6 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.
- Sun canza gida sau 18 a shekara uku saboda tsoron kyankyaso
- Mun kwato shanu 300 daga hannun barayi a dare daya – Gwamnan Zamfara
Daraktan Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, Chris Nikoi a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce, a kasashen Burkina Faso da Arewacin Kamaru da Chadi da Mali da Nijar da kuma Arewa maso Gabashin Najeriya akwai karin sababbin mutum miliyan biyar da ke bukatar agaji idan an kwantata da bara.
Hare-haren da mayakan jihadi ke kai wa sun haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira rashin tsaro da ba a taba ganin irin sa ba da ya raba mutum miliyan biyar da rabi da muhallansu.
Farashin kayan abinci ya rubanya, sannan ana samun karuwar yunwa mafi muni a shekara 10.
Majalisar ta ce yawaitar tashin farashin kayan abinci da rashin tsaro ke haddasawa a kasashen Sahel din na haifar da matsananciyar yunwa da karancin abinci a tsakanin al’umma, tana mai gargadin cewa mutum miliyan 29 da ke bukatar agajin ba wai a rubuce kawai suke ba, suna nan a zahiri kuma suna rayuwa cikin kunci.