Karar harbe-harbe, a babban ofishin ’yan sanda ya sanya zullumi a zukatan mazauna garin Aba na Jihar Abia.
Mazauna na cikin gudanar da harkokinsu a safiyar Alhamis a garin wanda ya yi fice wurin hada-hadar kasuwanci ne aka fara jin karar harbe-harben.
- Ramadan: Hanyar magance sabanin ganin wata —Farfesa Mansur
- Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda
- Ramadan: Za mu kwace lasisin duk wanda ya kara farashi —BUA
- An sake kai wa ofishin ’yan sanda hari a Imo
Tuni dai aka rufe hanyar zuwa ofishin tare da umartar mutane su koma gidajensu.
Wani babban jami’in ’in dan sanda ya tabbatar wa Aminiya cewa sun samu rahoto cewa maharan da suka kai farmaki a Hedkwatar ’Yan Sandan Jihar Imo na shirin kai hari a Babban Ofishin ’Yan Sandan na garin Aba.
Daga ranar Litinin zuwa Laraba, ’yan bindiga sun kai hare-hare hudu, uku a ofisoshin ’yan sanda, daya a gidan yari, inda suka saki fursunoni da tsararru kusan 2,000.
Maharan nan Imo sun kona motoci sama da 50 a Hedkwatar ’yan sandan Jihar.