✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana fargabar mutuwar yara da yawa a turmutsitsi a Ibadan

An kai yaran da suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a Ibadan.

Ana fargabar cewa yara da yawa ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da  aka yi a wani dandalin wajen wasan yara mai zaman kansa a makarantar Basorun Islamic High School da ke Ibadan a jihar Oyo.

Aminiya ta rahoton cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Prince Dotun Oyelade, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa da tura jami’an agaji domin taimakawa waɗanda abin ya shafa.

Ya kuma tabbatar da cewa an kai yaran da suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a Ibadan, da suka haɗa da Asibitin Patnas, Asibitin Western Hospital, Asibitin Jihar Ringroad, Asibitin ƙwararru na Molly da Asibitin Kwalejin Jami’a (UCH).

Oyelade ya yabawa Kwamishinan Lafiya, Dokta Oluwaserimi Ajetunmobi, bisa yadda ya bayar da agaji tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta tallafawa waɗanda abin ya shafa a cikin wannan mawuyacin lokaci.

Gwamnatin jihar ta kuma yi ƙarin haske kan cewa ba ta da hannu wajen shirya taron, ta kuma jaddada muhimmancin haɗa kai yadda ya kamata wajen shirya manyan bukukuwa, musamman waɗanda suka shafi yara da manya masu shekaru.

Ana dakon cikakken rahoto daga Kwamishinan ‘Yan sandan domin tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a wannan mummunan lamari.