Sama da mutum 20 ne ake fargabar sun kone kurmus bayan wata tankar man fetur ta kwace tare da fadawa cikin gadar Maboro da ke kogin Ankpa a jihar Kogi.
Rahotanni sun ce motar ta kwace wa direbanta ne sakamakon shanyewar birkinta, sannan ta fada cikin kogin.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 3:30 ya yammacin Laraba.
Sai dai ya ce mummunar konewar da wasu mutane suka yi ta yadda ba a iya gane su, ta sa zai yi wuya a tantance hakikanin adadin mutanen da suka rasu kawo yanzu.
Ya ce, “Ya zuwa yanzu babu wanda zai ce ga adadin mutanen da suka rasu, saboda akwai mutane da dama a cikin kogin lokacin da lamarin ya faru. Lamari ne da babu kyan gani. Ban taba ganin irinsa ba rayuwata,” inji Ahmed Usman, wani mazaunin garin na Ankpa.
Sai dai wani mazaunin garin da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce hatsarin shi ne irinsa mai muni a cikin watan nan.
Ya ce, “Wannan ne hatsari mafi muni. Sama da mutum 20 sun kone kurmus, wasu ma ko gane su ba a iya yi.”
Ya kuma ce wasu da dama kuma motar ta take su, sassan jikinsu kuma sun yi kaca-kaca, sai tsinto namansu aka rika yi.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a jihar, Stephen Dawulung, ya tabbatar da faruwar hatsarin, kodayake ya ce ba za a iya tantance hakikanin yawan mutanen da suka rasu ba.
Sai dai ya ce, “Yanzu haka jami’anmu na can suna aikin ceto. Ababen hawan da lamarin ya ritsa da su sun hada da tankar man da wata motar bas da kananan motoci guda uku da kuma babura guda uku.”