Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta fara farautar sojan da ya bindige masoyiyarsa mai suna Jennifer Ugadu a Jihar Bayelsa.
Mai magana da yawun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ranar Alhamis.
A wata sanarwa da ya fitar, Janar Nwachukwu ya ce rundunar ba za ta lamunta da kisan da aka yi wa matashiyar ba, sannan ya jajanta wa iyayenta.
- Buhari zai kaddamar da aikin shekara 40 a Katsina
- An rufe wasu hanyoyi a Katsina saboda zuwan Buhari
“Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta fara gudanar da bincike a kan lamarin, sai dai zuwa yanzu wanda ake zargin bai shiga hannu ba.
“An gina Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ne a bisa tsari da adalci kuma za ta ci gaba da kare hakkin dan-Adam wanda kundin tsarin mulki na 1999 ya tanadar,” inji sanarwar.
Ta kuma kara da tabbatar da al’umma cewar da zarar rundunar ta kammala bincike za ta sanar da sakamakon don yin adalci.
“Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na kara tabbatar da cewa ba za ta lamunci dukkan wani laifi ba, kuma irin wannan laifi dole ne a bincike shi a kuma gurfanar da wanda ya aikata,” inji Janar Nwachukwu.