Rahotanni daga Jihar Borno na cewa a halin yanzu ana gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a garin Damasak.
Majiyarmu ta tsaro ta ce sojoji sun ja daga suna kokarin fatattakar mayakan kungiyar ne bayan da suka shiga garin suna harbi kan mai uwa da wabi suna kone-kone.
- Boko Haram ta sake kwace garin Damasak
- Yadda bakin ciki ya yi ajalin iyayen ’yan matan Chibok 17
- Ban mutu ba, dogon suma na yi —Ummi Zee-zee
Wani babban jami’in tsaron sa-kai na CJTF, da ya tabbtar wa Aminiya cewa an shafe awa uku ana musayar wuta babu kakkautawa ya ce, “Mu taya sojoji da addu’a su samu murkushe shaidanun nan, Boko Haram sun sake dawowa Damasak, bayan harin da suka kai ranar Asabar; A taya sojojin da addu’a.”
Aminiya ta kawo rahoto cewa a ranar Talata, mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace garin suka kafa tutarsu, bayan da suka kuma kona caji ofis da cibiyoyin hukumomin agaji da asibiti da makaranta da gidaje da shaguna.
Majiyar tsaron da muka tuntuba kan yakin da ya kaure a safiyar Laraba ta ce, “Ina tabbatar maka cewa yanzu garin Damasak yana hannun sojoji, amma ana ci gaba da musayar wuta.
“Ka san a cikin kwanakin nan ’yan ta’adda sun kai hari a Damasak, amma ba za su yi nasara ba saboda sojoji sun yi tsayuwar daka domin su kare fararen hula”.