✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana cigiyar iyayen yaron da aka gano a Nasarawa

'Yan sanda sun bukaci wanda ya san yana da bayanan da za su taimaka waje gano iyayen yaron, a sanar da ofishin ’yan sanda mafi…

An tsinci wani yaro mai shekara tara mai suna Hassan Malam Tsalha, a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.

Sanarwar da Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Rahman Nansel, ya fitar ta ce, an tsinci yaron ne da misalin karfe 2:30 na dare ranar Litinin a hanyar Kwandare.

A cewar ’yan sanda, yaron ya ce shi dan Hadejiya ne a Jihar Jigawa kuma duk kokarin da suka yi don gano ahalinsa ya ci tura.

Daga nan jami’in ya bukaci duk wanda ke da bayanan da za su taimaka waje gano iyayen yaron, a sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa a jihar.