Mahukunta a Jihar Kebbi na gudanar da bincike a kan wasu da ake tuhuma da yi wa yarinya ‘yar shekara 3 fyade a cewar wani rahoto na Muryar Amurka.
Jam’in gudanarwa na Hukumar Kare Hakkin Bil’adama a jihar, Barrister Hamza Wala ya ce matasa biyu ne ake tuhuma da yi wa yarinya ‘yar shekara 3 fyade, kuma yanzu haka suna hannun hukumar tsaron ‘yan kasa ta ‘civil defence’ ana ci gaba da bincike.
- Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 8 a kauyen Filato
- ’Yan bindiga sun rufe Cibiyoyin kiwon lafiya 69 a Katsina
Hukumar tsaron ‘yan kasa ta ‘civil defence’ ta bakin kakakinta, Akeem Adeyemi ta ce lallai akwai magana mai kama da hakan da take bincike a kai, sai dai ba zata ce komai a kan batun ba, sai ta kammala bincike.
Ko bayan wannan, yanzu haka akwai wani matashi dan shekara 21 da ake zargin ya yi wa yarinya ‘yar shekara 6 fyade a garin Kalgo na jihar ta Kebbi wanda ‘yan sanda ke bincike akai.
Bisa ga la’akari da cewa Jihar kebbi na daga cikin jihohin da suka saka hannu ga dokokin kare ‘yancin yara idan bincike ya tabbatar da laifin wadanda ake tuhuma da yin fyade, akwai yuwuwar su kare sauran shekarun rayuwarsu a gidan kaso, muddin dai aka yi aiki da sabuwar dokar hukunta masu aikata fyade a jihar.
Kasashen duniya sun yi ta fafatuka da kashe makudan kudade wajen taimaka wa gwamnatoci a Najeriya a kokarin inganta dokokin kare ‘yancin kananan yara, wadanda sau da yawa suke fuskantar nau’o’in cin zarafi daban daban.
Duk da yake da yawa daga cikin gwamnatoci musamman na Arewa sun yi kwaskwarima tare da saka hannu ga dokokin kare ‘yancin kananan yara, har yanzu ana samun mutanen da ke yi wa dokokin karan-tsaye suna cin zarafin yara.
Sai dai har yanzu ana samun mutanen da ke kawar da kai daga dokokin kare ‘yancin kananan yara suna cin zarafin yara musamman ‘yan mata ta hanyar yi musu fyade, kamar wanda ya faru makon jiya a garin Yauri na Jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.