✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana binciken likita kan kashe budurwarsa

Danbaba ya ce abin takaici ne ganin wanda aka horas don ceto rayuwar jama'a ya koma mai kashe su.

Majisar Dokokin Jihar Kwara ta bukaci ’yan sanda su gudanar da bincike mai zurfi kan zargin kisan da ake yi wa wani likita a jihar.

Hakan ya biyo bayan korafin da Honarabul Abdullahi Danbaba, mai wakiltar Mazabar Kaiama ya gabatar wa majalisar yayin zamanta na ranar Alhamis.

Danbaba ya ce abin takaici ne ganin wanda aka bai wa horo don ceto rayuwar jama’a ya rikide ya koma mai daukan rai.

A watan Satumba ne aka cafke likitan a yankin Edo kan zargin kashe wani direban tasi sannan ya ci gaba da amfani da motarsa.

’Yan sanda sun ce bayan da aka zurfafa bincike, likitan ya yi ikirarin kashe wata budurwarsa a Jihar Kwara, wanda hakan ya sa ’yan sanda suka shiga bincike a Babban Asibitin Kaiama inda likitan ke aiki.

An yi zargin gano wasu gawarwaki biyu, daya an binne a ofishin likitan, daya kuma aka jefa a abin zuba shara.

Danbaba ya ce abin takaici ne ganin wanda aka bai wa horo don ceto rayuwar jama’a ya rikide ya koma mai daukan rai.