✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana binciken Dani Alves kan cin zarafin wata mata a gidan rawa

Ban taba ganin matar a rayuwata ba.

Wata kotu a Sifaniya na binciken tsohon dan wasan bayan tawagar kwallon kafa ta Brazil Dani Alves kan zargin cin zarafin wata mata a gidan rawa.

Kotun da ke Barcelona ta fara binciken ne a watan da ya gabata, bayan matar ta shigar da karar, tana mai zargin cewa ya sanya hannunsa a wani bangare na jikinta wanda bai kamata ba kuma ba tare da yardarta ba.

Duk da sanarwar ba ta fito karara ta ambaci sunan Alves ba, majiyoyi da dama sun tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa a kansa za a yi binciken.

’Yan sandan birnin Catalan sun ce matar ta shigar da karar ce a ranar 2 ga watan Janairu, sai dai Alves ya musanta zargin.

Duk da kuma Alves ya amince cewa ya halarci gidan rawar a ranar har ya cashe, sai dai ya ce bai taba ganin matar ba a rayuwarsa.