Gwamnatin Kaduna ta ce ta fara bincike kan matar da aka gani cikin wani bidiyo tana aman jini bayan an yi mata allurar rigakafin COVID-19.
Sannan gwamnatin ta Kaduna ta yi alkawarin bayyana sakamakon binciken ga jama’a.
- Mutum 2,000 muka karbo daga ’yan bindiga ta hanyar sulhu —Matawalle
- Dalibai mata sun yi wa maza fintinkau a Bauchi
- Dalibai mata sun yi wa maza fintinkau a Bauchi
- Mutum 1 ya rasu, 3 sun ji rauni a hatsarin mota
Aminiya ta rawaito, wata mata wadda bidiyonta ya karade kafafen sada zumunta tana aman jini bayan karbar rigakafin COVID-19, a Sakatariyar Kaduna.
Kwamishiniyar Lafiya ta Jihar, Dokta Amina Mohammed Boloni, ta sanar a ranar Alhamis cewa, cewarta, mutum 72,000 ne a jihar suka karbi rigakafin allurar, sai dai an samu mutum uku da suka shiga wani yanayi a sakamakon allurar.
“An yi wa mutum 72,000 rigakafin, kuma an samu mutum uku da suka shiga damuwa sosai a dalilin allurar. Da zarar an kammala bincike kan lamarin matar za a bayyana wa jama’a,” a cewar Boloni.