Sabon Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce ya gaji bashin da ya kai Naira biliyan 200 daga tsohuwar gwamnatin jihar.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a Jos, babban birnin jihar.
- Zan yi aiki tare da kai, Biden ya bai wa Tinubu tabbaci
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur?
Ya bayyana cewa, “A halin yanzu jihar nan na cikin bashin da ya haura Naira biliyan 200, inda bangaren kiwon lafiya ke bukatar kulawar gaggawa.
“Tsarin makarantunmu na bukatar gyara sosai, ababen more rayuwa sun lalace kuma a zahiri kowane bangare na bukatar gyaran gaggawa.
“Amma duk da dimbin bashin da jihar nan ke fama da shi a halin yanzu, hakan ba zai hana mu yi muku aiki yadda ya kamata ba.
“Mun himmatu ta hanyar samun kudaden shiga don yin ayyukan da suka dace.
“Dole ne na ce babu hanyoyin da za a magance wadannan kalubale cikin gaggawa, amma abu daya zan bayar da tabbataci, shi ne a shirye muke mu dauki kalubalen gaba-gaba don warware su.”