✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana amfani da sunana na bogi a shafin Twitter – IBB

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida (ritaya), ya ce akwai masu amfani da sunansa da hotunansa na bogi a shafin sadarwa na zamani Twitter. Babangida…

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida (ritaya), ya ce akwai masu amfani da sunansa da hotunansa na bogi a shafin sadarwa na zamani Twitter.

Babangida ya sanar da hakan ne, a wani jawabin da mataimakinsa na musamman Zubairu Abdulrauf ya fitar inda ya ce, Tsohon shugaban bai da wani shafin sadarwa dake da alaqa da wannan shafin da ake yadawa, don haka ya buqaci jama’a da su yi watsi da wannan zargin.

Kamfanin dillancin labarai NAN ne ya fitar da rahoton yau Talata a Minna.