Hukumar Zaɓen Jihar Yobe (SIEC) ta sanar da ɗage zaɓen ƙananan hukumomin da ta shirya gudanarwa a ranar 25 ga Mayun 2024.
Hukumar ta ce ta ɗage zaɓen zuwa ranar Asabar, 8 ga watan Yunin bana kuma a wannan rana yaƙin neman zaɓe ya ƙare kamar yadda ka’idojin zaɓen suka tanadar.
- Kwamishinoni 3 sun yi murabus a Ribas
- Ƙungiyar Ƙwadago ta yi watsi da N48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Shugaban hukumar, Dokta Mamman Mohammad ne ya sanar da hakan ga manema labarai a yau Laraba a Damaturu, babban birnin Yobe.
A cewarsa “zaɓen ranar 25 ga watan Mayu 2024 da aka shirya a baya ba zai yiwu ba sakamakon rashin kammala tanadar kayan aiki da wasu dalilai da za su iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin cikin gaskiya da adalci.
“Saboda haka ya zama wajibi a ɗage zaɓen zuwa ranar 8 ga watan Yunin 2024. Makonni biyu ke nan bayan ranar 25 ga Mayu.
“A jadawalin mu, canje-canjen za su kasance ne kaɗai a ranar zaɓen da lokacin dakatar da yaƙin neman zaɓe, amma za a sanar da sakamakon zaɓen da zarar an kammala kamar yadda aka tsara.”
Sanarwar ta ce hukumar tana bai wa jama’a haƙuri dangane da wannan canjin lokaci da aka samu.