✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishinoni 3 sun yi murabus a Ribas

Dangantaka na ƙara yin tsami tsakanin ɓangaren Ministan Abujan, da Gwamna Fubara.

Ƙarin wasu kwamishinoni uku sun ajiye aikinsu yayin da suka miƙa takardun murabus daga Majalisar Zartarwa ta Jihar Ribas.

Kwamishinoni sun haɗa da na ilimi, Farfesa Chinedu Mmon, da na gidaje, Gift Worlu da kuma na muhalli, Austin Ben Chioma.

Bayanai sun ce kwamishinonin sun ajiye muƙamansu saboda abin da suka kira “hatsarin da ke cikin ayyukansu.”

Kwamishinonin waɗanda masu biyayya ne ga tsohon gwamnan jigar, Nyesom Wike – su ne kwamishinoni na bayan nan da suka ajiye muƙamansu bayan tsamin dangantaka tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon gwamna Wike.

Cikin wata wasiƙa da ya aike wa gwamnan ta hanyar ofishin sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo, tsohon Kwamishinan Ilimin ya ce ya ajiye muƙaminsa ne saboda wurin aikinsa ba shi da daɗi.

Wannan lamari na zuwa ne makonni bayan wasu kwamishinonin da ke goyon bayan Wike su ma suka miƙa takardar murabus ɗinsu.

Kwamishinonin su ne Farfesa Zacchaeus Adangor, wanda ya ajiye muƙamin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a, da Isaac Kamalu, wanda ya sauka daga kujerar Kwamishinan Kuɗi.

A baya-bayan nan dai dangantaka na ƙara yin tsami tsakanin ɓangaren Ministan Abujan, da Gwamna Fubara.

A ranar Litinin ne gwamnan ya zargi tsohon gwamnan da bar wa jiharsa tilin bashi, bayan sauka daga mulki.

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamna Fubara ya bayyana aniyar bincikar gwamnatin Wike wanda a lokacin ya riƙe muƙamin Babban Akantar jihar ta Ribas.