✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni Da Manyan Sakatarori A Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya rantsar da Kwamishinoni  biyu da Shugaban Ma’aikata da Manyan Sakatarorin hudu, da masu ba da shawara na…

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya rantsar da Kwamishinoni  biyu da Shugaban Ma’aikata da Manyan Sakatarorin hudu, da masu ba da shawara na musamman guda 28.

Sabbin kwamishinonin da aka nada sun hada da Farfesa Abba Idris da Alhaji Mohammed Bara.

Gwamnan ya umarci sabbin kwamishinonin da su bayar da tasu gudummawar wajen tsarawa da aiwatar da dukkan manufofi, shirye-shirye da ayyukan gwamnati cikin tsanaki da gaskiya don amfanin jama’ar jihar.

“Har ila yau, ana sa ran ku yi amfani da ƙwarewarku da kuma cusa sabbin dabaru don ƙara kima ga nasarorin da wannan gwamnatin ke samu.

“Yya kamata ku lura da fara yi wa jama’a hidima tare da la’akari sosai ga makomar jihar,” in ji Buni.

Da yake jawabi ga sabon shugaban ma’aikata Hamidu M. Alhaji, gwamnan ya ce “jihar tana rasa kwararrun ma’aikata sakamakon yin ritaya, ya kamata ku samar da sabbin ma’aikata masu inganci don yi wa jama’armu hidima.

“Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnati za ta ba wa ofishinku duk wani tallafi da ya dace don horar da ma’aikata don samun  ingantaccen aiki.

“Ina gargadinku da cewar, wannan gwamnatin ba za ta amince da nuna fifiko wajen nada mukamai da karin girma ga wadanda ba su cancanta ba, musamman ta wajen yin watsi da wadanda suka cancanta.

“Dole ne mu yi iya iyawar mu don duba cancanta don sa ma’aikatan gwamnati su kasance masu inganci,  dole ne mu bambanta tsakanin ma’aikatan gwamnati musamman ta yin la’akari da kwarewa” in ji shi.

Gwamna Buni ya umarci sabbin masu ba da shawara na musamman da su fahimtar da  mutanensu dangane da manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa.

“Yawancin lokuta, an bar al’ummominmu a baya saboda mun kasa kawo su kusa da mu don fahimtar manufofi da shirye-shiryen gwamnati da take yi masu ma’ana.

“Ofishin mai ba da shawara na musamman zai iya kasancewa mai ƙarfi ne kawai idan akwai haɗin gwiwar ta yadda za ku rika samun damar samun ingantattun bayanai, don ku ba da shawara ta hanyar kyakkyawar fahimta.”

Gwamna Buni ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kiyaye manufofinta na bude kofofinta ga jami’an gwamnati don ba da gudummawar da ta dace.

Don haka ya umurci sabbin ma su bada shawarar da su sanya hannu a cikin manufofin da ake bi wajen tabbatar da gaskiya da kuma bayyana gaskiya a gwamnatinsa. In ji Buni.

Bayan Nan ne kuma sai Gwamnan ya  rantsar da shugaban hukumar kula da ayyukan koyarwa Yakubu Dokshi, da wasu mambobi uku na hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, da kuma mamba a ma’aikatan kananan hukumomin jihar.