Hukumomin Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane uku da aka samu da laifin ta’addanci.
Biyu daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisa ’yan Saudiyya ne, dayan kuma dan kasar Yemen ne wanda aka bayyana a matsayin dan Houthi da ke yaki da kawancen da Saudiyya ke jagoranta tsawon shekaru.
- ‘Yan siyasa 9 za su janye wa Ahmed Lawan takarar Shugaban Kasa —Orji Kalu
- El-Rufai ya haramta zanga-zanga a Kaduna saboda batancin da aka yi a Sakkwato
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce Daya daga cikin mutanen mamba ne na wata Kungiyar ’yan ta’adda, da aka samu da makamai da abubuwan fashewa a gidansa.
An samu dayan dan kasar Saudiyya da laifin hannunsa a kisan wani mai gadi kamar yadda BBC ya ruwaito.
An zargi dan kasar Yemen da shiga Saudiyya ba bisa ka’ida ba da nufin kai hare-haren ta’addanci.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha suka kan yadda ake gudanar da shari’a a Saudiyya.