Hankalin jama’a ya tashi a yankin Karmo da ke Abuja bayan an zargi ’yan asalin yankin da yunkurin kona kasuwar garin a ranar Talata.
Kasuwar garin Karmo da ke matsayin daya daga cikin mafiya hada-hada a Yankin Birnin Tarayya, ta fuskanci matsalar gobara har sau uku, inda na baya-bayan nan ya auku a karshen watan Maris da ya gabata.
- Sam ba da Nafisa nake maganar tarbiyya ba – Sarkin Waka
- DAGA LABARA: Yadda Za A Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya —Masana
Wani mazaunin garin mai suna Sani Aliyu ya shaida wa Aminiya cewa tun bayan aukuwar gobarar bayan, an yi ta samun takun saka a tsakanin ’yan kasuwar da suka rasa shagunansu na wacin gadi kamar 300 a bangare guda da kuma jagororin ’yan asalin garin a daya vangaren, kan rashin amincewarsu da sake kafa shagunan.
“Da farko sun bukaci da a rusa kwamitin shugabancin kungiyar ’yan kasuwar tare da maye gurbinsu da wasu, duk da cewa babu ’yan kabilar yankin a ciki, inda ’yan kasuwar suka amince da bukatarsu.
“Sai dai duk da haka sun ki amincewa da a sake mayar da rumfunan kan ikirarin cewa akwai wurarensu na tarihi a wajen da sauran barazana iri-iri.
“To ana cikin wannan hali ne sai ga wuta ta tashi a daya daga cikin shagunan kasuwar da suka tsira a yayin gobarar baya.
“Wutar ta fara ci da misalin karfe 12 da rabi na daren Litinin, sannan bayan ’yan banga da sauran jama’a sun shawo kanta, sai aka gano cewa an watsa man fetur a jikin wasu shaguna da ke iyaka da inda wutar ta tashi, sai kuma wasu abubuwan tsafi da aka binne.”
Sani ya ce wadannan dalilan ne suka fusata matasa tare da yunkurin garzayawa zuwa fadan Dagacin garin da nufin cinna mata wuta a safiyar Talata.
Sai dai ya ce jagororin ’yan kasuwar sun shawo kan matasan gabanin aikata ta’asar.
Yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Abuja kan lamarin bai samu nasara ba, kasancewar ba ta amsa waya da ya buga mata ba ko amsa sako da ya aika mata, gabanin rubuta labarin.